Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa

Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa

- Jami'iyyar APC ta raba kayan abinci cike da manyan motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa da mabuƙata a jihar Zamfara

- Tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari ne ya bayyana haka a Gusau, babban birnin jihar, lokacin da jam'iyyar ta ƙaddamar da fara rabon kayan

- APC ta jinjina ma shuwagabannin Jam'iyyar jihar musamman Yari da Marafa da suka haɗa kansu don cigaban APC

Jam'iyyar APC reshen jihar Zamfara ta ce ta shirya raba kayan abinci na kimanin manyan motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa a jihar Zamfara saboda zuwan watan Ramadan.

KARANTA ANAN: Sarkin Musulmi Ya umarci al'umar Musulmi su nemi jinjirin watan Ramadan ranar Litinin

Tsohon gwamnan jihar, Abdul'aziz Yari da shugaban APC na jihar ne suka bayyana haka a wajen ƙaddamar da fara rabon kayan a Gusau, babban birnin jihar.

Jam'iyyar ta kaddamar da fara rabon kayan abincin ga talakawa a ranar Lahadi.

Abdul'aziz Yari wanda Sanata Kabir Marafa ya wakilta ya ce kayan abincin sun haɗa da; Manyan motocin ɗaukar kaya 54 cike da buhunan shinkafa, Motoci 32 ɗauke da buhunan sikari, Motoci 22 ɗauke da buhunan masara da kuma 22 ɗauke da Gero.

Ya ƙara da cewa za'a rarraba kayan abincin ne a dukkan ƙananan hukumomi 13 da jihar Zamfara ke da su.

Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa Saboda Ramadan
Zuwan Ramadana: APC ta raba kayan Abinci cike da Manyan Motocin ɗaukar kaya 130 ga talakawa Saboda Ramadan Hoto: @AA_Yari2015
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce:

"Kowacce ƙaramar hukuma zata samu motoci 10, wanda suka haɗa da motocin shinkafa biyu, motar sikari ɗaya, motar masara ɗaya da motar Gero ɗaya."

"Sai kuma ƙaramar hukumar Gusau wadda itace babban birnin jihar zata samu Motocin abinci 10, wanda idan ka haɗa duka zai baka 75."

KARANTA ANAN: Malamin Islamiyyan da ya yi wa Dalibi dukan da ya yi doguwar suma, ya shiga hannun ‘Yan Sanda

Yari ya ƙara da cewa ragowar motoci 55 kuma za'a rarraba su ne ga marayu, mutane masu buƙata ta musamman, hukumomin tsaro, da dai sauran su.

A jawabinsa ya ce, suma shuwagabannin jam'iyya da kuma manyan jam'iyya zasu shiga cikin waɗanda zasu amfana.

Daga ƙarshe Yari ya jinjina ma shugabannin APC na jihar misamman a sasancin da suka yi kwanan nan tsakaninsa da Marafa.

Sanata Abba Aji, wanda shine ya wakilci uwar jam'iyya ta ƙasa a wajen taron, ya jinjina ma shuwagabannin APC na jihar kan wannan halin dattako da suka nuna.

Ya ce: "Na jinjin ma Yari da Marafa kan wannan ƙudirin nasu da kuma haɗa kan su da suka yi don cigaban jam'iyya."

A wani.labarin kuma 'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Rundunar Yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar kuɓutar da wasu mutane 11 da yan bindiga suka sace.

Kakakin yan sandan jihar ne ya bayyana haka, ya kuma ce an samu wannan nasara ne saboda ƙoƙarin gwamnan jihar, Bello Matawalle, na dawo da zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Tags:
APC
Online view pixel