Duk lalacewar Mulkin Jonathan Najeriya bata lalace ba, yanzu ma ba zata lalace ba, Ahmad Lawan

Duk lalacewar Mulkin Jonathan Najeriya bata lalace ba, yanzu ma ba zata lalace ba, Ahmad Lawan

- Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan ya ce babu yadda za'ai Najeriya ta faɗi, ta lalace a yanzun tunda har bata lalace a zamanin mulkin Jonathan ba

- Lawan ya yi wannan jawabi ne a wajen ƙaddamar da shirin koyon sana'a da kuma samar da aikin yi a mazaɓar sanatoci ta Katsina ta tsakiya

- Ya ƙara da cewa bazai taɓa yuwu wa wai saboda matsalar tsaron da muke fama da ita ace Najeriya zata lalace ba, shin mun mance ne da lokacin da aka sa dokar ta baci a yankin arewa maso gabas

Shugaban majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawan, ya ce ƙalubalen tsaro da gwamnatin yanzun ke fuskanta bazai sa ace ƙasar ta lalace ba.

Lawan ya faɗi haka ne a ya yin da yake ƙaddamar da shirin samar da aikin yi wanda mutane 2000 suka amfani dashi a mazaɓar Katsina ta tsakiya.

KARANTA ANAN: Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

A watan Disamban shekarar data gabata, jaridar Financial Times ta bayyana cewa Najeriya na kan hanyar wargajewa.

Jaridar kasuwancin ta ƙasa-da-ƙasa ta ƙara da cewa ƙalubalen tsaro da ƙasar ke fama dashi ya tsayar da cigaban tattalin arziƙinta wanda wannan babban ƙalubale ne kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Hakanan a ranar Jumu'an da ta gabata, ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar hamayya ta PDP, ta ce Najeriya na tafiya a hankali zuwa lalacewa matuƙar wannan matsalolin rashin tsaron ya cigaba da faruwa.

Duk lalacewar Mulkin Jonathan Najeriya ba lalace ba, Yanzu ma ba zata lalace ba, Ahmad Lawan
Duk lalacewar Mulkin Jonathan Najeriya ba lalace ba, Yanzu ma ba zata lalace ba, Ahmad Lawan Hoto: @DrAhmadLawan
Asali: Twitter

Amma shugaban Sanatocin ya ce duk masu irin wannan tunanin "Sun manta da halin da ƙasar ta baro ne."

Lawan ya ce "Najeriya bata lalace ba a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, saboda haka bazai yuwu ta lalace a yanzun ba."

KARANTA ANAN: Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga

"Duk waɗanda ke cewa wannan yanayin da muke ciki na rashin tsaro zai sa ƙasar nan ta lalace, ta wargatse, ko kuma tana kan hanyar hakan, to lallai sun manta abunda ya faru a baya ne. Najeriya ba zata taɓa wargatsewa ba.

Hakanan kum shugaban sanatocin ya ce, idan sun mance ne to su tuna cewa a zamanin GEJ ne aka saka dokar ya ɓaci a yankin arewa maso gabas."

"Amma Najeriya bata lalace ba, sabida haka a yanzun ma ba zata lalace ba." Inji Ahmad Lawan.

Mutum mai daraja ta uku a ƙasar nan ya yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su haɗa karfi da ƙarfe da gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari wajen ƙanin an yaƙi matsalar tsaro ta yaƙi ci yaƙi cinyewa.

A wani.labarin kuma 'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara

Rundunar Yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar kuɓutar da wasu mutane 11 da yan bindiga suka sace.

Kakakin yan sandan jihar ne ya bayyana haka, ya kuma ce an samu wannan nasara ne saboda ƙoƙarin gwamnan jihar, Bello Matawalle, na dawo da zaman lafiya a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel