'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara

'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara

- Rundunar Yan sanda reshen jihar Zamfara ta bayyana samun nasarar kuɓutar da wasu mutane 11 da yan bindiga suka sace

- Kakakin yan sandan jihar ne ya bayyana haka, ya kuma ce an samu wannan nasara ne saboda ƙoƙarin gwamnan jihar, Bello Matawalle, na dawo da zaman lafiya a jihar

- Hakanan Kuma, Jami'an yan sanda a jihar sun fatattaki wata tawagar yan bindiga da suke kan hanyar su na kai hari a Kauyen Yarkala dake jihar

Rundunar yan sanda a jihar Zamfara ta bayyana cewa ta kuɓutar da mutane 11 daga hannun yan bindiga a jihar, Punch ta ruwaito.

Kakakin runduɓar ta yan sandan jihar, SP Muhammad Shehu ne ya faɗi haka a wani jawabi da ya fitar ranar Asabar a Gusau, babban Birnin jihar.

KARANTA NAN: Sheikh Ahmad Gumi: Ganin Ƴan Bindiga Ya Fi Ganin Buhari Sauƙi

Ya ce a ranar 9 ga watan Afrilu hukumar yan sanda tare da taimakon ma'aikatar tsaron cikin gida ta jihar sun kuɓutar da wasu mutane 11 da wata tawagar yan bindiga ta sace.

Muhammad Shehu ya ce yan bindiga sun tasa waɗanda suka kama ɗin zuwa wani daji a Gobirawan Chali dake yankin ƙaramar hukumar Maru.

Kakakin yan sandan ya ce 10 cikin mutane 11 da aka kuɓutar ɗin sun fito ne daga sassa daban-daban na faɗin jihar Zamfara, ragowar mutum ɗaya ya fito daga jihar Kaduna.

'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara
'Yan Sanda sun kuɓutar da Mutane 11 da aka sace, Sun fatattaki Yan Bindiga a Jihar Zamfara Hoto: @mobilepunch
Asali: Twitter

Ya ce nasarar kuɓutar da mutanen na cikin kudirin gwamnan jihar, Bello Matawalle, na tattaunawar Zaman lafiya da ake cigaba da yi.

KARANTA ANAN: Mun yarda sojoji mata su sanya Hijabi idan zai karesu daga harsashi: Kungiyar CAN

Ya kuma ƙara da cewa duk kan mutanen da aka kuɓutar ɗin an miƙa su ga ma'aikatar tsaron cikin gida waɗanda ke da alhakin haɗa su da iyalansu.

A wata nasarar ta daban, kakakin yan sandan jihar ya ce jami'ai sun fatattaki wasu yan bindiga d suka kai hari ƙauyen Yarkala dake ƙaramar hukumar Bungudu, kuma sun kwato muggan makamai.

"A ranar 8 ga watan Afrilu, jami'an yan sanda na 'operation Puff Adder' sun fatattaki yan bindiga bayan samun labarin tawagar yan bindiga ta nufi ƙauyen Yarkala zasu kai hari." Inji Muhammad Shehu.

Ya ƙara d cewa A ya yin korar yan ta'addan jami'an yan sanda sun kwato bindiga ƙirar Ak-47 tare da jaka mai ɗauke da harsasai.

A wani labarin kuma An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta

Wani dalibi na kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kogi ya tsinci kansa cikin matsala sakamakon daukar bindiga da yayi zuwa makaranta

Hukumomin tsaro na iya gurfanar da dalibin bayan sun kammala bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262