An Kama Mutumin da ke Sa Mata a Mota Ya Masu Bidiyo Tsirara

An Kama Mutumin da ke Sa Mata a Mota Ya Masu Bidiyo Tsirara

  • Rundunar 'yan sandan Birnin Tarayya (Abuja) ta damke wani mutum mai suna Usman Mohammed bisa zarginsa da cin zarafin mata da yi masu barazana a birnin Abuja
  • Wanda ake zargin da ke gudanar da sana'a a Abuja, ya yaudari wata mace zuwa motarsa inda ya ci zarafinta ya kuma dauki hotunan tsaraicinta don yi mata barazana
  • Kwamishinan 'yan sanda CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya jaddada aniyarsu ta kama kowane irin mai laifi ya kuma bukaci al'umma da su riqa kai masu rahoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Rundunar 'yan sandan yankin Babban Birnin Tarayya (Abuja) ta samu nasarar kama wani mutum mai suna Usman Mohammed da ake zargi da cin zarafin mata da gudanar da barazana a tsakanin mata a yankin Lugbe da ke Abuja.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun je har gida sun harbe shugaban Miyetti Allah

Jami’an 'yan sanda daga shiyyar Lugbe karkashin jagorancin DPO ne suka gudanar da samamen da ya kai ga cafke shi a ranar Juma’a, 6 ga Nuwamba, 2026, bayan samun rahoton laifin da ake zarginsa da aikatawa.

Usman Mohammed da aka kama
Wanda ake zargi da cin zarafin mata a Abuja. Hoto: FCT Abuja Command
Source: Facebook

Jami'ar yada labaran rundunar, SP Josephine Adeh ta fitar da sanarwa a Facebook a ranar 11 ga Nuwamba, 2026 game da kama shi.

Wanda ake zargin ya yi kokarin guduwa ne lokacin da ya hango jami'an 'yan sandan a yankin FHA Lugbe, amma suka bi shi suka rike shi kafin ya shiga babbar hanya.

Binciken da 'yan sanda suka yi

Binciken farko ya nuna cewa Usman Mohammed yana amfani da dabarar ba da bashi don tsara mata, musamman mata masu takaba da sauran matasa masu rauni.

A cikin danyen aikin da ya yi kwanan nan, ya yaudari wata mace zuwa cikin motarsa ya kai ta wani wuri mai nisa a Lugbe, inda ya ci zarafin ta tare da gudanar da lalata da ita.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Ya tilasta mata tsirara tare da daukar bidiyon sassan jikinta na sirri, wanda ya yi amfani da su wajen yi mata barazanar tona mata asiri a fili ko kashe ta.”

Kara karanta wannan

'An harbi motar Atiku Abubakar da ya je kamfen,' Sanata Dino Melaye

Usman na hannun 'yan sanda

A yanzu haka wanda ake zargi yana hannun 'yan sanda ana gudanar da bincike mai zurfi a kansa, kuma za a mika shi ga kotu dumu-dumu da zarar an kammala bincike.

Kwamishinan 'yan sandan FCT, CP Ahmed Muhammed Sanusi, ya yi Allah-wadai da kowane irin nau'in cin zarafi ko yi wa mata barazana, yana mai kiran mazauna birnin da kada su yi shiru.

A maimakon haka, ya bukaci su rika sanar da 'yan sanda kowane irin laifi ta hanyar lambobin gaggawa: 08032003913 ko 08061581938.

Taswirar Abuja a Najeriya
Taswirar FCT Abuja a Najeriya. Hoto: Legit
Source: Original

An kashe shugaban MACBAN

A wani labarin kun ji cewa tsagerun 'yan bindiga da ake zargi da zama barayi sun kashe shugaban kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na karamar hukumar Takum a jihar Taraba.

An harbe mamacin ne a kofar gidansa da ke unguwar Abuja a Takum tsakanin karfe 7:00 zuwa 8:00 na daren Lahadi bayan ya dawo daga kasuwar shanu.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun gudu nan take bayan harbin ba tare da daukar komai ba, lamarin da ya jefa tsoro da fargaba a tsakanin al'ummar yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng