Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba

- Hukumar dake shirya jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara sayar da fom ranar Asabar ɗin da ta gabata

- JAMB ta dakatar da fara yin rijistar ne tun baya saboda wasu matsaloli da ba'a yi tsammani ba a kan lambar zama ɗan ƙasa NIN

- Akwai sabbin dokoki da hukumar ta ɓullo da su a wannan shekarar wanda doƙe saika cika su kan ka yi rijista

Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB ta sanar da fara yin rijistar jarabawar ta 2021 ranar Asabar.

KARANTA ANAN: An shiga firgici yayin da aka kama wani dalibin Najeriya da bindiga a harabar makaranta

Hukumar ta sanar da fara rijistar zana jarabawar neman gurbin shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) da kuma rijistar DE.

Hukuncin fara rijistar yazo ne awanni 48 bayan hukumar ta dakatar da shirin saboda wasu matsaloli data samu kan lambar zama ɗan ƙasa NIN.

Amma a wani saƙo da mai magana da yawun JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya fitar ya ce an warware matsalar saboda haka yanzun an fara rijistar.

Dalla-Dalla yadda zaka yi rejistar jarawar ta bana ba tare da matsala ba.

1. Ka tambatar da kana da Lambar waya da E-Mail

Yana da matuƙar muhummanci ya kasance kana da lambar waya, da kuma E-mail masu aiki ba tare da tangarɗa ba. Saboda kowanne ɗalibi na da buƙatar turawa da kuma amsar saƙo daga JAMB a ya yin gudaɓar da rijistar sa.

2. Lambar jikin ƙatin ɗan kasa wato NIN

JAMB ta maida amfani da NIN ya zama wajibi g duk mai son zana jarabawar a wannan shekarar. Sabida haka ya zama wajibi ka mallake ta kafin ka yi rijista.

Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba
Dalla-Dalla: Yanda zaka yi rijistar JAMB 2021 ba tare da samun Matsala ba Hoto: punchng.com
Asali: Twitter

3. Ka ziyarci shafin JAMB

Bayan ka tabbatar da ka mallaki email da NIN, saika ziyarci shafin JAMB, ka buɗe ma kanka kundin aje bayanai kafin kaje ka siya takardar rijista ɗin.

KARANTA ANAN: Ba zamu zuba ido muna Kallo ana kashe mana Mutane a Kudu ba, Sanata Babba kaita ya yi kakkausan Gargaɗi

4. Ka duba cancantar ka na zana jarabawar bana a JAMB iBass

Bayan ka buɗe kundin aje bayananka a shafin JAMB, akwai buƙatar ka duba shafin don tabbatar da shin ka cancanci ka zana jarabawar ta bana, zaka iya duba wannan a 'JAMB iBass' dake shafin na JAMB.

5. Sai kuma ka sayi Lambar sirri wadda zata baka damar yin rijista.

Bayan ka tabbatar da ka cancanci ka zauna jarabawar ta wannan shekara, sai kuma kaje ka siya lambar sirri (JAMB E-PIN) waɓda zata baka damar yin rijista, zaka iya siyan E-PIN din a bankuna ko a wuraren da hukumar ta amince da su.

5. Cibiyar CBT

Bayan kammala dukkan haka, saika ziyarci ɗaya daga cikin wuraren zana jarabawa a na'ura mai ƙwawalwa (CBT Centre) waɗanda JAMB ɗin ta tantance kuma ta amince da su tare da dukkan bayanan ka da kuma PIN ɗin daka siya don yin rijista.

A wani labarin kuma Gwamnan CBN ya bayyana babban dalilin da yasa Shugaba Buhari ke yawan ciyo bashi

Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN), Dr. Godwin Emefiele ya bayyana babban dalilin da yake tilasta gwamnati ta ciyo bashi

Gwamnan ya ce ciwo bashi ba laifi bane kuma ba zunubi bane, amma akwai wajabcin sanya ido a kan ƙuɗin da aka amso da kuma hanyar da aka yi amfani da su.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel