An ba Tinubu Satar Amsa daga Siyasar Jonathan domin Nasara a 2027 cikin Sauƙi

An ba Tinubu Satar Amsa daga Siyasar Jonathan domin Nasara a 2027 cikin Sauƙi

  • Kungiyar NDI-ABAT ta shawarci Shugaba Bola Tinubu da kada ya dogara da gwamnoni wajen neman sake lashe zaben shugaban kasa na 2027
  • Kungiyar ta bukaci Tinubu ya koyi darasi daga faduwar Goodluck Jonathan a zaben 2015 saboda dogaro da gwamnoni da masu rike da mukaman siyasa
  • Ta kuma bukaci shugaban kasar ya karfafa alaka kai tsaye da 'yan Najeriya tare da fadada tasirin APC a yankin Kudu maso Gabas

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Umuahia, Abia - Wata kungiyar siyasa mai suna Ndigbo for Asiwaju Bola Ahmed Tinubu (NDI-ABAT) ta shawarci Shugaba Bola Tinubu da kada ya mayar da gwamnonin jihohi ginshikin shirin sake zabensa a shekarar 2027.

Kungiyar ta bukaci shugaban kasar ya gina kyakkyawar alaka kai tsaye da al'ummar Najeriya tare da karfafa wasu hanyoyin samun goyon bayan siyasa da ba su dogara da masu rike da mukaman gwamnati ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon yadda aka tallafa wa Tinubu yana tafiya a wurin taro ya dauki hankali, Sowore ya yi magana

An ba Tinubu shawara ta ɗauki darasi a siyasar Jonathan
Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Goodluck Jonathan, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

An ba Tinubu shawara kan siyasa

Ta ce ya kamata Tinubu ya yi nazari kan abin da ya faru da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, wanda ya sha kaye a zaben 2015 bayan dogaro da gwamnonin jihohi da manyan 'yan siyasa, cewar Punch.

A wata sanarwa da kodinetan kungiyar na kasa, Mazi Okechukwu Isiguzoro, da shugaban kwamitin amintattunta, Dim Uche Okwukwu, suka sanya wa hannu, kungiyar ta ce bai kamata shugaban kasa ya dauki goyon bayan 'yan siyasa a matsayin tabbataccen abu ba.

NDI-ABAT ta yi zargin cewa wasu gwamnonin da ke nuna goyon bayansu ga Tinubu a bainar jama'a, a boye suna taimakawa 'yan takarar jam'iyyun adawa.

Ta bayyana cewa akwai yiwuwar wasu shugabannin siyasa su rika nuna biyayya ga shugaban kasa a fili, yayin da a zahiri suke yi wa abokan hamayyarsa aiki a boye.

Ana neman Tinubu ya koyi darasi a siyasar Jonathan
Tsohon shugaban kasa a Najeriya, Goodluck Jonathan. Hoto: Goodluck Jonathan.
Source: Twitter

Gargadin da kungiyar ta yi wa Tinubu

Kara karanta wannan

"Abin da zai sa Tinubu ya samu gagarumar nasara a zaben shugaban kasa na 2027"

Kungiyar ta bukaci Bola Tinubu ya yi nazari sosai kan darussan siyasar zaben shugaban kasa na 2015, musamman yadda rashin kyakkyawan tafiyar da kawance da sauran manyan 'yan siyasa zai iya kawo masa matsala.

A cikin sanarwar, kungiyar ta ce:

"Shawarar da muke ba Shugaba Tinubu a bayyane take: Kada ya sake maimaita kura-kuran siyasa da aka danganta da zaben 2015. Kada ya dogara matuka da gwamnonin jihohi, sannan kada ya dauki goyon bayan da ake nunawa a fili a matsayin tabbacin biyayya.
"Kada ya mika makomarsa ta siyasa ga muradun gwamnonin daidaikun mutane. Maimakon haka, ya gina alaka mai fadi da 'yan Najeriya tare da karfafa wasu hanyoyin siyasa masu zaman kansu kafin zaben 2027.
"Kawance a siyasa yana da muhimmanci, amma bai kamata ya maye gurbin hulda kai tsaye da al'umma ba."

NDI-ABAT ta kuma nuna damuwa kan yiwuwar wasu gwamnonin da ke goyon bayan Tinubu a yanzu su sauya matsayinsu yayin da matsin lambar siyasa da bukatun sake zabensu ke karuwa.

Ta ce shugaban kasar ya kamata ya iya bambance tsakanin furucin goyon baya da ake yi a bainar jama'a da kuma sahihiyar biyayya da za ta dore har zuwa lokacin zabe, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Sarakunan Yarbawa a jihohin Arewa 19 sun dauki babban alkawari ga Tinubu

Jonathan ya goyi bayan yan APC

An ji cewa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nuna goyon bayansa ga ’yan takarar APC a Bayelsa bayan rasa takarar shugaban kasa.

Jonathan ya ce ’yan takarar za su iya wakiltar al’ummominsu yadda ya kamata, tare da bayar da gudunmawa wajen ci gaban Bayelsa.

Ya kuma bukaci ’yan takarar da sauran masu ruwa da tsaki su tabbatar da zaman lafiya, hadin kai da ci gaba a jihar Bayelsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.