Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga

Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga

- An ruwaito cewa, wani sojan ya 'yan bindiga suka yi garkuwa dashi ya kubuta daga hannunsu

- S.K Usman ya wallafa cewa, sojan ya kwance damarar daya daga cikin 'yan bindigan inda ya hallaka biyu daga cikinsu

- An sace sojan ne tun ranar 24 ga watan Fabrairun wannan shekarar a hanyarsa ta zuwa Kebbi

Wani sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi a ranar 24 ga watan Fabrairu kan hanyarsa ta zuwa hutu jihar Kebbi ya kubuta bayan share kwanaki a hannun 'yan bindiga.

Kakakin rundunar sojin Najeriya S.K Usman ne ya wallafa labarin kubutar jarumin sojan a shafinsa na Tuwita.

KU KARANTA: A yau kasar Saudiyya za ta fara duban watan Ramadana mai zuwa

Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga
Sojan ruwa da aka yi garkuwa dashi ya kubuta, ya kuma hallaka 'yan bindiga Hoto: @skusman
Asali: Twitter

Legit.ng Hausa ta ruwaito inda S.K Usman ke nuna farin cikinsa da kubutar sojan da cewa:

"Labari mai dadi, wani gwarzo ma'aikacin sojan ruwa na Najeriya, Ak Bala, wanda wasu lokuta aka yi garkuwa da shi a ranar 24 ga Fabrairu 2021, a kan hanyarsa ta zuwa Kebbi hutu, ya samu nasarar kubuta.

"Ya yi nasarar kwance damarar daya daga cikin masu garkuwar, sannan ya yi amfani da makaminsa ya kashe biyu daga cikinsu ya tsere."

KU KARANTA: Duk da umarnin hani daga kotu, masaurautar Kano ta fara yanka filin Idin 'Yar Akwa

A wani labarin, A wani kai hari ta sama da kuma amfani da bindigogin atilare, sojojin Najeriya sun kawar da manyan shugabannin kungiyar 'yan ta'addan ISWAP da dama a jihar Borno.

An kai hare-haren ne ta jiragen sama da ba za a iya tantance su ba bayan mako guda da bacewar jirgin NAF Alpha.

An tattaro cewa harin da aka kai kan manyan maboyar ISWAP guda uku a Kusuma, Sigir a Ngala da Arijallamari a cikin kananan hukumomin Abadam, sun kashe shugabanni biyu ‘yan ta’adda Amir Abu-Rabi da Mohamer Likita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel