Caccakar gwamnati ta fi ta'addanci da 'yan bindiga hatsari, Fadar shugaba Buhari

Caccakar gwamnati ta fi ta'addanci da 'yan bindiga hatsari, Fadar shugaba Buhari

- Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya ce baya ga rashin tsaro, Najeriya tana fama da caccaka daga jama'a ko ta ina

- A cewarsa, wasu sun sadaukar da lokutansu wurin caccakar gwamnati ba tare da ganin kokarinta ba ko kadan

- A cewarsa, kushe shugabanci ya fi rikicin bangarori, garkuwa da mutane, ta'addanci, shan jini, rashin tsaro da kuma kashe-kashe muni

Femi Adesina, kakakin shugaban kasa ya ce ba matsalar rashin tsaro kadai Najeriya take fama da ita ba, tana fuskantar "yakin harsuna".

A cewar Adesina, caccaka da kushe da wannan gwamnatin take fuskanta ya yi yawa. Wasu mutane sun sadaukar da rayuwarsu wurin runtse ido daga ganin wani amfani da kokarin wannan gwamnatin.

Ya bayyana wannan tunanin nasa a wata wallafa da ya fitar a Facebook ranar Alhamis, inda ya gabatar da matsalolin da Najeriya take fuskanta na rashin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki kuma yaja kunnen masu kushe akan kada su yi amfani da damar da aka basu na tofa albarkacin bakunansu wurin zagin gwamnati.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Ribas

Caccakar gwamnati ta fi ta'addanci da 'yan bindiga hatsari, Fadar shugaba Buhari
Caccakar gwamnati ta fi ta'addanci da 'yan bindiga hatsari, Fadar shugaba Buhari. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: 2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu

"Yanzu haka kasarmu tana fama da matsaloli da dama. Najeriya tana fuskantar ta'addanci, rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makamai, kashe-kashe da kuma caccaka da kushe," kamar yadda ya wallafa.

"Caccaka da kushe Sabuwar matsala ce? A'a, dama ta dade kuma tafi duk wasu matsaloli wuyar magani. Ta zarce ta'addanci, rashin tsaro, garkuwa da mutane, fashi da makamai da kashe-kashe da sauransu zama gagarumar matsala.

"Kushe da caccaka sun cutar da Najeriya, shugabancinta, duk wani ma'aikacin gwamnati . Idan ka kuskura ka hau wani mukami, karami ko babba, za ka fuskanci matsaloli kuma zaka zama makiyinsu.

"Duk kokarinka babu wanda zai gani. Ta yuwu kayi kokari kwarai a soja, ka zama janar, ka shugabanci PTF kuma kayi bajimta, yanzu kuma kayi shugabancin kasa a matsayinka na farar hula har sau biyu, ga kushe da caccaka daga harsuna iri-iri kuma duk wasu jaridu suna wallafa mara kyau dangane da kai.

"Kullum kushe da caccaka a Najeriya yana kara yawaita, kuma tun daga Muhammadu Buhari har zuwa kananun kujeru na gwamnati, babu wanda ba a suka.

"Sannan duk wasu masu kiran kansu masu rajin kare hakkin bil'Adama, 'yan jaridu suna wallafa abubuwan da suka ga dama, gidan talabijin ba a barsu a baya ba, kafafen sada zumuntar zamani ma sun rike wuta sannan duk wani wanda yake rike da babbar waya da 'yan siyasa suna yadda suka ga dama.

"Sannan hatta malaman addinai suna wa'azi akan duk abinda suka ga dama, suna burin sanya tsana tsakanin al'umma."

A wani labari na daban, hukumar jami'an tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta azabtar da Sa'idu Afaka, direban shugaban kasa Muhammadu Buhari har hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin hukumar na kasa, Dr Peter Afunanya, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ta ranar Laraba da yamma, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tazo: "Hukumar DSS ta musanta labarin kanzon kuregen da Saharareporters tayi ta yadawa na azabtar da Sa'idu Afaka, direban Shugaban kasa na musamman har yayi sanadiyyar mutuwarsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel