DSS tayi martani akan zarginta da ake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari

DSS tayi martani akan zarginta da ake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari

- Hukumar DSS ta musanta azabtar da direban shugaba Muhammadu Buhari, Sa'idu Afaka har ta kai ga mutuwarsa

- Kakakin DSS, Dr Peter Afunanya ya sanar da hakan a wata takarda da suka saki da yammacin Laraba

- Kamar yadda takardar tazo, DSS bata kama Afaka ba balle har ta azabtar dashi kamar yadda labarin yayi ta yawo

Hukumar jami'an tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta azabtar da Sa'idu Afaka, direban shugaban kasa Muhammadu Buhari har hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin hukumar na kasa, Dr Peter Afunanya, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ta ranar Laraba da yamma, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tazo: "Hukumar DSS ta musanta labarin kanzon kuregen da Saharareporters tayi ta yadawa na azabtar da Sa'idu Afaka, direban Shugaban kasa na musamman har yayi sanadiyyar mutuwarsa.

KU KARANTA: Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama

DSS tayi martani akan zarginta daake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari
DSS tayi martani akan zarginta daake da tsarewa tare da azabtar da marigayin direban Buhari. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Ku tsammaci cigaba a fannin tsaro nan babu dadewa, Mukaddashin sifeta janar Alkali

"Babu wanda ya kama Afaka balle har DSS ta rike shi har ta kai ga azabtar dashi ya mutu.

"Hukumar tana matukar yin adalci ga duk wanda aka zarga kamar yadda doka da salon demokradiyya suka tanadar."

Idan ba a manta ba, hadimin shugaban kasa na harkar yada labarai na musamman, Mallam Garba Shehu ya sanar da mutuwar Afaka tun ranar 6 ga watan Afirilun 2021 bayan ya dade yana fama da ciwo, kuma ya tura ta'aziyyar shugaban kasa zuwa ga iyalansa.

"Don haka ana bukatar jama'a da suyi fatali da duk wasu karairayi da wasu za su yada a kafafen sada zumunta."

A wani labari na daban, Shugaban karamar hukumar Kumbotso dake jihar Kano, Hassan Garban Kauye Farawa, ya dauki hadimai 55.

Daily Trust ta ruwaito cewa, yayin da yake rantsar dasu, Farawa ya ce ya yi hakan ne don tabbatar da manufar Gwamna Abdullahi Ganduje na fatattakar fatara a jihar.

Ya horesu da su zage damtsensu wurin aiwatar da duk wasu ayyuka da zasu kawo cigaba ga karamar hukumar.

"Daukar hadimai 55 yana daya daga cikin hanyar fatattakar talauci daga jihar Kano na Gwamna Abdullahi Umar Ganduje musamman ga matasa a wannan halin tsanani da wahala da ake ciki," a cewarsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel