2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu

2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu

- Bola Tinubu, shugaban jam'iyyar APC na kasa yana cigaba da bin hanyoyi cikin salo irin na siyasa don tsayawa takarar shugabancin kasa a 2023

- Akwai wasu 'yan siyasa kuma shugabannin jam'iyyar PDP da zasu dage kuma su zage wurin tabbatar da sun dakatar dashi daga cimma manufarsa

- Wadannan jiga-jigan jam'iyyar PDP din zasu yi amfani da karfinsu, jama'arsu da kuma matsayinsu a arewa don dakatar dashi

Yayin da shugaban jam'iyyar APC na Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu yake bin dabaru da salo iri-iri na siyasa don ganin ya cimma burinsa na tsayawa takarar shugabancin kasa tunda 2023 tana karatowa.

Sai dai akwai jiga-jigan jam'iyyar PDP masu fadi a ji, kuma masu matukar karfi da jama'a a arewacin Najeriya da zasu tsayu don su dakatar dashi.

Cikinsu akwai Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto, Gwamna Bello Muhammad Matawalle na Zamfara da kuma Atiku Abubakar.

KU KARANTA: Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes

2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu
2023: Tambuwal da sauran 'yan siyasa da zasu iya zama kalubale ga cikar burin Tinubu. Hoto daga @SMOHSokoto, @Bellomatawalle, @atiku, @AsiwajuTinubu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

Tabbas dole ne Tinubu ya fuskanci Tambuwal, Atiku da Matawalle a 2023. Babu shakka jihar Sokoto ta dade tana da cikin APC musamman a arewa saboda jam'iyyar ce ta mamaye arewa.

Aminu Tambuwal

Tambuwal dan jam'iyyar APC ne kafin 2018 tayi ya canja sheka zuwa PDP, sannan a wannan shekarar ya tsaya takarar shugabancin kasa.

Bello Matawalle

Bayan Matawalle ya samu nasara a takarar da yayi a 2019 yayin da APC ta jihar taki yin zaben fitar da gwani, ya lashi takobin makalewa a kujerarsa a Zamfara kamar yadda wanda ya sauka mulkin, Abdulaziz Yari, yayi.

'Yan siyasa da dama sun yarda da cewa APC zata dage wurin kwato jihar daga hannun APC saboda kada arewa ta rasa jihar a zaben 2023.

Atiku Abubakar

Dama Atiku Abubakar ya taba hawa kujerar mataimakin shugaban kasa, kuma ya tsaya takarar shugabancin kasa a 2019, ana sa ran ba zai zubar da makamansa ba har sai ya samu nasara.

Don haka matsawar Tinubu yana so ya dare kujerar shugaban kasa sai ya yi yaki da duk wadannan 'yan siyasan masu karfin gaske.

A wani labari na daban, Hope Uzodimma, gwamnan jihar Imo, ya ce akwai wasu 'yan siyasa da suke da hannu a harin ofisoshin 'yan sanda da kuma gidajen gyaran hali a jihar.

A cewarsa, 'yan siyasan sun yi hakan ne musamman don tayar da tarzoma a mulkin jam'iyyar APC.

Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da ake tattaunawa dashi a gidan talabijin din Channels.

Asali: Legit.ng

Online view pixel