Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban karamar hukuma a Ribas
- Miyagun 'yan bindiga sun kai farmaki inda suka sace shugaban karamar hukumar Okrika na jihar Ribas
- Lamarin ya auku ne a titin Peter Odili inda 'yan bindiga suka yi awon gaba da Honarabul Philemon Kingoli
- A wannan daren ne wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne suka kai farmaki wani otal a Fatakwal
Wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.
Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.
Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar, Nnamdi Omoni, har yanzu bai riga ya tabbatar da aukuwar lamarin ba.
KU KARANTA: Sojin Najeriya sun mamaye garinsu ministan Buhari, suna zuba ruwan wuta
KU KARANTA: Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama
Har ila yau, an kashe mutum biyu a ranar Laraba yayin da wasu suka samu raunika yayin da 'yan bindigan da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne suka kai farmaki wani otal dake kan titin Victoria a Fatakwal.
Wannan cigaban ya kawo tsananin tsoro da tashin hankali ga mazauna tsohon birnin Fatakwal wanda hakan yasa wasu suka fara gudu don ceton rayukansu.
A halin yanzu, rundunar 'yan sandan jihar ta tura wasu 'yan sanda yankin domin tabbatar da doka da oda.
A wani labari na daban, sabon sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali ya ce 'yan sanda a karkashin mulkinsa zasu tabbatar da bunkasa harkar tsaro a Najeriya.
Ya kara da bada tabbacin fifitawa da kuma tabbatar da 'yan sandan jihohi a karkashin mulkinsa.
IGP ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Abuja bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nada shi.
Shugaba Muhammadu Buhari ya daura Alkali a kujerar sifeta janar na 'yan sandan Najeriya, inda ya maye gurbin Mohammed Adamu wanda ya kamata ya sauka daga madafin iko a watan Fabrairu, saidai an kara masa watanni 3.
Asali: Legit.ng