Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa

Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa

- Gwamna Matawalle na jihar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London a matsayin kaiwa arewa hari

- Tun watan Maris shugaba Buhari ya tafi London don a duba lafiyarsa kuma dama tunda ya dare kujerar shugaban kasa yake zuwa London akai-akai

- Wasu 'yan Najeriya mazauna London sun yi zanga-zanga a can kuma sun yi hakan ne bisa yadda likitocin Najeriya suke yajin aiki gwamnati ta nuna musu halin ko-in-kula

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya kwatanta zanga-zangar da 'yan Najeriya mazauna London suka yi wa Shugaba Muhammadu Buhari a matsayin hari ne aka kaiwa arewa.

Tun a cikin watan Maris shugaban kasa ya bar Najeriya ya wuce London don a duba lafiyarsa.

Dama Buhari ya tsiri zuwa London tun da ya hau kujerar shugaban kasa a 2015, The Cable ta ruwaito.

Wasu 'yan Najeriya mazauna London sun yi wa Buhari zanga-zanga bisa yajin aikin da likitocin Najeriya suke yi a Najeriya.

KU KARANTA: Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo

Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa
Matawalle: Zanga-zangar da aka yi wa Buhari a London farmaki ne ga arewa. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

A wata takarda ta ranar Alhamis wacce Matawalle ya tura ya bayyana zanga-zangar a matsayin al'amari da wasu suka dauki nauyi, kuma wadanda suka shirya basu da wayewa.

Ya kuma ja kunne akan kaiwa 'yan arewa hari da kuma sana'arsu a kudu.

"Na yi Allah wadai ta yadda kullum ake nuna tsana ga dan arewa kuma hakan ya zarce har suka kaiwa Buhari hari saboda masu zanga-zangar ba zasu iya boye tsana da hassadar da suke yi wa 'yan arewa ba.

"Duk yadda suke fushi, abinda suka yi bai dace da dabi'a da wayewa da mutunci ba. Yanzu haka tsanar shugaban kasa da arewa tana kara yawaita a garesu. Gaskiya yin hakan bai dace ba ko kadan kuma daga masu zanga-zangar har masu daukar nauyinsu basu da wata daraja.

"Na tabbatar da shugaban kasa dan kudu ne ba zasu yi masa haka ba, kuma sun yi hakan ne musamman don su wulakanta shugaban kasa sakamakon ganin yawan 'yan Najeriyan da suke zama a London." Matawalle yace.

KU KARANTA: Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya

A wani labari na daban, hukumar jami'an tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta azabtar da Sa'idu Afaka, direban shugaban kasa Muhammadu Buhari har hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Kakakin hukumar na kasa, Dr Peter Afunanya, ya bayyana hakan a wata takarda da ya fitar ta ranar Laraba da yamma, The Nation ta ruwaito.

Kamar yadda takardar tazo: "Hukumar DSS ta musanta labarin kanzon kuregen da Saharareporters tayi ta yadawa na azabtar da Sa'idu Afaka, direban Shugaban kasa na musamman har yayi sanadiyyar mutuwarsa."

Asali: Legit.ng

Online view pixel