Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo

Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo

- Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana babban dalilin da ya sanya Shugaba Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon IGP

- Kasancewar akwai mutane da dama wadanda suka cancanci hawa wannan kujerar, Osinbajo ya ce Alkali yafi dukansu matsayi

- Har yanzu Buhari yana Turai ana duba lafiyarsa sakamakon hakan ne mataimakinsa, Farfesa Osinbajo ya jagoranci nadin

A ranar Laraba mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana dalilin da ya sanya Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon sifeta janar na 'yan sanda.

A cewar Osinbajo, Alkali yafi kowannensu matsayi, hakan ne ya bayar da damar da ya sanya aka nada shi a matsayin sabon IGP din.

Mataimakin shugaban kasa ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Abuja yayin da yake nada Alkali a sabuwar kujerar.

KU KARANTA: Jerin sunaye da tushen dukiyar mutane mafi arziki 10 na duniya daga mujallar Forbes

Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo
Dalilin da yasa Buhari ya nada Usman Alkali a matsayin sabon shugaban 'yan sanda, Osinbajo. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

Buhari da ya zabi Alkali yanzu haka yana Turai ana duba lafiyarsa.

"Zabenka da Shugaban kasa yayi ya bi hanyoyi da dama bayan tantance duk DIGP da AIGP tukunna. Ya zabeka ne saboda kaine babba kuma wanda yafi cancanta a cikinsu," cewar Osinbajo.

"Bari in mika maka sakon taya murna a matsayinka na sabon IGP, kuma dama ana irin wannan tantancewar yayin nada sabon Sifeta janar a lokacin da wa'adin wanda yake kan kujerar ya kare.

"Wannan nadin wanda ake duba cancanta da matsayi zai tabbatar da cewa ka cancanta da kujerar da za a dauraka kuma kana da horo isasshe da zai baka damar gudanar da ayyukanka a sabon matsayinka.

"Kafin in cigaba, ina mika godiyata ga tsohon sifeta janar. Sakamakon daukan tsawon lokaci wurin yi wa Najeriya da 'yan Najeriya ayyuka tukuru. Muna godiya kuma 'yan Najeriya suna godiya."

KU KARANTA: Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

A wani labari na daban, sabon sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali ya ce 'yan sanda a karkashin mulkinsa zasu tabbatar da bunkasa harkar tsaro a Najeriya.

Ya kara da bada tabbacin fifitawa da kuma tabbatar da 'yan sandan jihohi a karkashin mulkinsa.

IGP ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Abuja bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nada shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel