Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya

Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya

- Baya ga rike manyan mukamai, 'yan siyasa sun dade suna samun nadin sarauta iri-iri a fadin kasar nan

- Yayin da wasu suke alfahari da sarauta kwaya daya rak, akwai masu rike da sarautu 6 na gargajiya

- A wannan labarin akwai sunayen 'yan siyasa 10, ciki har da tsofaffin gwamnoni da shugabannin kasa masu sarauta

A Najeriya, 'yan siyasa suna samun damar rike kujerun sarautar gargajiya daga garuruwansu da inda ba garinsu ba.

Suna samun wadannan matsayin ne sakamakon yadda aka lura da ayyukansu a unguwanni da kasar baki daya.

A wannan rubutun zan kawo sunayen tsofaffin 'yan siyasa, ciki har da tsofaffin gwamnoni da shugabannin kasa wadanda aka nada a matsayin shugabannin gargajiya.

1. Shugaba Muhammadu Buhari

Kusan shekaru 7 da suka shude, Enyi din Aba dake jihar Abia, mai martaba Eze Isaac Ikenne, ya baiwa shugaba Muhammadu Buhari, wanda a lokacin dan takarar shugaban kasa ne sarauta. Ya nada shi matsayin Ogbuagu 1 na kasar Ibo, ma'ana makashin zaki, alama ta gwarzontaka.

Sannan a 2018 buhari ya kara samun wata sarautar da 'Ikeogu 1 na kasar ibo (ma'ana mai yi wa Ndi Ibo fada) a karamar hukumar Bende dake jihar, wacce take da fiye da shugabannin gargajiya 60 a mazabar Isuikwuato/Umunneochi.

Sarkin Daura, Umar Faruk a 2015 ya nada Buhari a matsayin Bayajidda na masarautar Daura, a garinsa dake jihar Katsina.

Sarkin Gwandu kuma shugaban sarakunan Kebbi, Alhaji Muhamamdu Bashar ya nada Buhari a matsayin sadauki Gwandu.

Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya
Fitattun 'yan siyasa 10 a Najeriya masu sarautar gargajiya. Hoto daga @Thenation
Source: Twitter

KU KARANTA: Hotunan Zulum yana gwangwaje 'yan gudun hijira da N200m da kayan abinci a Bama

2. Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan

Shugabannin gargajiyan Igbere sun nada shi 'Nwanne Di Na Mba' (Dan uwan hulda) 1 na masarautar Igbere.

3. Sanata Rochas Okorocha

Ya wakilci Imo ta yamma, kuma masarautar kudu, gabas da arewa, wacce shugaban sarakunan kudu yake jagoranta, Eze (Dr.) Ezo Ukandu JP da kuma mai girma Alhaji Muhammadu Maccido (CFR) suka nada shi "Owelle Ndi Igbo" da "Dan Jekan Sokoto".

Okorocha yana da sarauta a kasar Yarabawa ta Okala na Ehue; Talban Gwagwalada da Uban Talakawa.

4. Orji Uzor Kalu

Yafi kowa sarauta a garin Ihechiowa, dake karamar hukumar Abia ta arewa sakamakon bunkasa garin da yayi. Sannan shine "Ikenga Ata Igbo-Ukwu Umuzomgbo Ihechiowa".

5. Femi Fani-Kayode

Ya rike kujerar ministan sufurin jiragen sama kuma masarautar Shinkafi dake Zamfara ta nada shi "Sadaukin Shinkafi".

6. Asiwaju Bola Ahmed Tinubu

Shine jigo kuma jagorana jam'iyyar APC na Najeriya. Yana rike da sarautar Jagaban na masarautar Borgu dake jihar Nej, Aare na Ile-Oluji da Aare Ago na kasar Egba.

7. Atiku Abubakar

A 1982, sirikinsa, basaraken Adamawa, Alhaji Aliyu Mustafa ya nada tsohon mataimakin shugaban kasan a matsayin Turakin Adamawa.

Sannan a 2017, an kara nada shi a matsayin Wazirin Adamawa yayin da aka mayar da Turakin Adamawa ga dansa.

8. Goodluck Jonathan

Sarkin Bauchi, Rilwanu Suleiman Adamu ya nada tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan sarautar "Jigon Bauchi". An yi masa wannan nadin kuma an sanya wa titin Sabon Kaura zuwa titin Miri sunansa.

9. Sunday Dare

An nada ministan wasanni da matasa a matsayin Agbaakin na Kasar Ogbomoso dake jihar Oyo. Soun din Ogbomoso, Obo Jimoh Oyewumi ne ya nada shi.

10. Hon Shina Peller

Alaafin din Oyo, Oba (Dr) Lamidi Okayiwola Adeyemi III, ya nada shi Ayedero ba kasar Yarabawa. Wanda Peller ne mai Club Quilox sannan kuma dan majalisar wakilai ba mazabar Iseyin/Itesiwaju/Iwajowa/Kajola na jihar Oyo.

KU KARANTA: Dan Najeriya ya wallafa hotunan bishiyar mangwaro a kauyensu da ke samar da 'ya'ya 10,000

A wani labari na daban, sabon sifeta janar na 'yan sanda, Usman Alkali ya ce 'yan sanda a karkashin mulkinsa zasu tabbatar da bunkasa harkar tsaro a Najeriya.

Ya kara da bada tabbacin fifitawa da kuma tabbatar da 'yan sandan jihohi a karkashin mulkinsa.

IGP ya bayyana hakan ne a gidan gwamnati dake Abuja bayan mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya nada shi.

Source: Legit

Online view pixel