Duk da batan jirgin sojin sama, sojoji sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP

Duk da batan jirgin sojin sama, sojoji sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP

- Biyo bayan batan jirgin yakin sojin saman Najeriya, sojoji sun fatattaki da dama daga cikin 'yan ISWAP

- Harin ya yi sanadiyyar mutuwar wasu da dama daga ciki har da shugabannin 'yan ta'addan na ISWAP

- An kuma kwato wasu kayayyaki da suka hada da bindigogi da dama daga hannun 'yan ta'addan

A wani kai hari ta sama da kuma amfani da bindigogin atilare, sojojin Najeriya sun kawar da manyan shugabannin kungiyar 'yan ta'addan ISWAP da dama a jihar Borno.

An kai hare-haren ne ta jiragen sama da ba za a iya tantance su ba bayan mako guda da bacewar jirgin NAF Alpha.

An tattaro cewa harin da aka kai kan manyan maboyar ISWAP guda uku a Kusuma, Sigir a Ngala da Arijallamari a cikin kananan hukumomin Abadam, sun kashe shugabanni biyu ‘yan ta’adda Amir Abu-Rabi da Mohamer Likita.

Hakazalika an kashe kuma masu gadinsu da mayakansu da dama.

KU KARANTA: El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafe a doron kasa

Duk da batan jirgin sojin sama, sojojin sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP
Duk da batan jirgin sojin sama, sojojin sun yi kaca-kaca da mambobin ISWAP Hoto: dailypost.ng
Asali: UGC

Yayin da Abu-Rabi ke lura da karbar haraji a madadin kungiyar ISWAP a yankin Tafkin Chadi, Likita kuwa na cikin kwamandojin da ke kula da hare-hare kan sojojin.

An kai samamen ne a karkashin rundunar sojin sama na Operation Lafiya Dole tare da hadin gwiwar sassan aiki na Artillery na 3, na MNJTF.

Wani jami’in leken asirin soja ya fada wa PRNigeria cewa Kusuma cibiya ce ta shugabannin ISWAP yayin da Sigir da Arijallamari ke a matsayin sansanin horar da ‘yan ta’adda.

Majiyar ta ce: “Wasu daga cikin hare-haren na baya-bayan nan a Damasak, Malam Fatori, Munguno, Dikwa da Marte an hade su ne daga yankunan.

"Hare-hare ta sama da ruwan bama-bamai a kan sansanin ISWAP sun tursasa 'yan ta'adda da suka tsira da raunuka zuwa yankunan Jibularam da Sabon Tumbu da ke gabar kogi."

A halin da ake ciki, Sojojin Najeriya tare da tallafin jami'an sa kai na JTF sun yiwa ‘yan ta’adda kwanton bauna a kan hanyar Gubio-Magumeri.

Sojojin sun kafa tarko ne a kauyen Kareram lokacin da suka samu bayanan sirri na 'yan ta'addan da ke tuka babura da ke tafe daga Kauyen Malam Yaumari don kai hari.

Yayin da aka kashe wasu daga cikin ‘yan ta’addan wasu kuwa sun tsere da munanan raunuka.

Kayayyakin da aka kwato daga hannun ‘yan ta’addan sun hada da manyan makamai da babura da sauransu

KU KARANTA: Dangote, wasu fitattu sun ba da makudan miliyoyi a bikin littifin Aisha Buhari

A wani labarin, Sojojin Najeriya sun rusa maboyar 'yan ta'addan da suka kaiwa sojoji hari a kusa da kauyen Bonta tare da dage al'ummomin da ke karamar hukumar Konshisha a jihar Benuwe a jiya.

An kuma ce sojojin sun kashe wasu 'yan bindiga 12 da suke mambobin kungiyar da ta kai wa sojojin hari, TVC ta ruwaito.

Al'umar Bonta sun kasance cikin rikici tare da jama'ar Ukpute-Ainu na karamar hukumar Oju a kan filaye, lamarin da ya sa gwamnati ta aje sojoji don sintiri a yankin don wanzar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel