Sojoji sun afkawa mafakar 'yan ta'adda, sun kashe 12 sun kwato makamai

Sojoji sun afkawa mafakar 'yan ta'adda, sun kashe 12 sun kwato makamai

- Sojojin Najeriya sun kai samame mafakar wasu 'yan ta'adda, inda suka kashe 'yan bindiga 12

- Samamen ya biyo bayan harin da 'yan ta'addan suka kai sojojin kwantar da tarzoma a wani yankin Benue

- Sai dai, rundunar 'yan sanda ta jihar Benue ba ta tabbatar da faruwar lamarin ba zuwa lokacin hada wannan rahoton

Sojojin Najeriya sun rusa maboyar 'yan ta'addan da suka kaiwa sojoji hari a kusa da kauyen Bonta tare da dage al'ummomin da ke karamar hukumar Konshisha a jihar Benuwe a jiya.

An kuma ce sojojin sun kashe wasu 'yan bindiga 12 da suke mambobin kungiyar da ta kai wa sojojin hari, TVC ta ruwaito.

Al'umar Bonta sun kasance cikin rikici tare da jama'ar Ukpute-Ainu na karamar hukumar Oju a kan filaye, lamarin da ya sa gwamnati ta aje sojoji don sintiri a yankin don wanzar da zaman lafiya.

Idan za a iya tunawa, a ranar Litinin da yamma, sojojin da aka tura don wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummomin biyu da ke rikici sun kasance suna sintiri a kusa da Kauyen Bonta lokacin da aka ba da rahoton cewa ‘Bonta Boys’ sun yi musu kwanton-bauna.

KU KARANTA: Wani tsohon Sanatan jihar Filato ya riga mu gidan gaskiya jiya Talata

A lokacin da kura ta lafa, an tattaro cewa ‘yan dabar Bonta Boys sun kame wasu daga cikin sojojin bisa hujjar cewa (sojojin) sun lalata haramtattun shingayensu.

A lokacin hada wannan rahoto, mazauna Kauyen Bonta da kewaye duk sun kaurace wa kauyukansu kuma a yanzu haka suna samun mafaka a Tse-Agbaragba, hedikwatar karamar Hukumar Konshisha.

Lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO), DSP Catherine Anene ta ce ba ta da labarin wannan samamen da sojoji suka kai a karamar hukumar ta Konshisha.

Kokarin jin ta bakin kwamandan rundunar Operation Whirl Stroke (OPWS), Manjo Janar Adeyemi Yekini ya ci tura saboda dukkan layukansa suna kashe a lokacin wannan rahoton.

KU KARANTA: Tsawon mako guda kenan Korona ba ta yi kisa ba a Najeriya

A wani labarin, Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hyacinth Nwiye, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a karamar hukumar Khana a jihar Rivers.

Kakakin jam'iyyar, Ogbonna Nwuke, ya bayyana cewa an sace Nwiye ne a daren ranar Lahadi 4 ga watan Afrilu a gidansa da ke Khana kamar yadda PM News ta ruwaito.

Nwuke ya ce: "Wasu mutane da ba mu san ko su wanene ba sun sace shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a karamar hukumar Khana a jihar Rivers a gidansa, ranar Lahadi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel