El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafesu daga doron kasa

El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafesu daga doron kasa

- Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana matsayinsa kan yadda ya kamata a bi da 'yan bindiga

- A cewarsa, duk wani dan bindiga ya rasa lasisin zama lafiya a Najeriya, dole a shafe shi

- Ya kuma bukaci gwamnatin Najeriya da ta nemo hanyoyi don yin maganin 'yan bindiga

Gwamna Nasir El-rufai na jihar Kaduna ya ce 'yan bindiga da ke addabar Najeriya sun rasa 'yancin su na rayuwa a karkashin tsarin mulki kuma dole ne a shafe su adoron kasa, The Guardian ta ruwaito.

El-rufai ya bayyana haka ne a yayin wani taron zauren gari kan tsaro na kasa wanda Ma’aikatar Yada Labarai da Al’adu ta shirya a Kaduna mai taken: “Kawo Mafita don Ingantawa da Hadin Kan Kasa a Najeriya”.

”‘Yan bindiga suna yaki da Najeriya kuma babu wata hanya da za ta tunkari wannan fitina ta yanzu sai dai kawai jami’an tsaro su yaki ‘yan bindiga tare da kwato dazuzzukan da suke zaune.

KU KARANTA: Jerin jami'an da suka rike matsayin Sufeta-Janar na 'yan sanda daga 1999 - 2021

El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafe a doron kasa
El-Rufai: 'Yan bindiga sun rasa 'yancin rayuwa, dole ne a shafe a doron kasa Hoto: theguardian.ng
Asali: UGC

"Hukumomin tsaro galibi suna martani ne kan matsalar barayi da satar mutane, muna cikin yaki ne tare da wadannan 'yan ta’adda da ke kalubalantar ikon mallakar kasar Najeriya.

“Dole ne jami’an tsaron mu su hada kai don yaki da 'yan bindiga da ‘yan ta’adda, da kuma dawo da dazuka domin baiwa 'yan kasa masu bin doka da oda damar yin halattaccen noma da kiwo.

El-rufai ya bayyana cewa babu wanda ke da wani mukami, da zai musanta bukatar ci gaba, kan yaki da masu aikata laifuka.

Ya kara da cewa, kara kaimin tsaro shine zai gurgunta masu aikata laifuka tare da kwantar da hankalin talakawa.

Ya ce dole ne gwamnati ta gano tare da yin maganin masu ta da hankalin 'yan kasa Najeriya.

KU KARANTA: Da dumi-dumi: 'Yan bindiga sun saki mambobin Cocin RCCG 8 da suka sace a Kaduna

A wani labarin daban, Sojojin Najeriya sun rusa maboyar 'yan ta'addan da suka kaiwa sojoji hari a kusa da kauyen Bonta tare da dage al'ummomin da ke karamar hukumar Konshisha a jihar Benuwe a jiya. A

n kuma ce sojojin sun kashe wasu 'yan bindiga 12 da suke mambobin kungiyar da ta kai wa sojojin hari, TVC ta ruwaito.

Al'umar Bonta sun kasance cikin rikici tare da jama'ar Ukpute-Ainu na karamar hukumar Oju a kan filaye, lamarin da ya sa gwamnati ta aje sojoji don sintiri a yankin don wanzar da zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel