Yajin Aikin Likitoci: 'Yan majalisa sun fusata, sun baiwa Shugaban MDCN awa 24 ya bayyana gabansu

Yajin Aikin Likitoci: 'Yan majalisa sun fusata, sun baiwa Shugaban MDCN awa 24 ya bayyana gabansu

- Kwamitin majalisar dokokin ƙasar nan baiji daɗin rashin halartar shugaban hukumar kula da likitoci (MDCN) zuwa wajen taron da suka gayyace shi ba

- Yan majalisar dake cikin kwamitin sun yi matuƙar fusata, sun bashi awanni 24 ya bayyana gabansu ko kuma su bada umarnin kamo shi

- An dai tura ma shugaban gayyata ne yazo ya yi cikakken bayani akan yajin aikin da likitocin ƙasar nan ke yi

Kwamitin majalisar wakilai kan harkokin kiwon lafiya ya yi barazanar bada izinin kamo shugaban hukumar dake kula da likitocin ƙasar nan (MDCN), Tajudeen Sanusi, matuƙar bai bayyana a gabansu ba gobe Jumu'a.

An gayyaci Sanusi da ya bayyana a gaban kwamitin domin ya amsa wasu tambayoyi akan yajin aikin da ƙungiyar likitoci (NARD) ke yi.

KARANTA ANAN: NSCDC ta kama makiyaya 50 da muggan Makamai a wasu Jihohin ƙasar nan

Sai dai bisa dole yan majalisar wakilan dake cikin kwamitin suka ɗage taron bayan sun samu masaniyar cewa Sanusi na can ya halarci kotun hukumarsa.

Kotun dai ita ce wajen da ake yin hukunci a hukumar MDCN kuma tana da matsayin babbar kotu, tana hukunci ne akan likitoci idan bukatar hakan ta taso.

Shugaban kwamitin, Hon. Tanko Sununu ya ce Sanusi bai girmama gayyatar mu ba wacce take ta gaggawa amma yaje can ya halarci abinda ransa ke so.

Yajin Aikin Likitoci: 'Yan majalisa sun fusata, Sun baiwa Shugaban MDCN awa 24 Ya bayyana gabansu
Yajin Aikin Likitoci: 'Yan majalisa sun fusata, Sun baiwa Shugaban MDCN awa 24 Ya bayyana gabansu Hoto: @HouseNGR
Asali: Twitter

Ɗan majalisa Sununu ya ce:

"Mun aika da gayyatar mu ga dukkan masu ruwa da tsaki da su halarci wannan taron, amma sai aka yi rashin sa'a shi yaƙi zuwa."

"Saboda shine ginshiƙin taron, dole tasa muka ɗage taron daga yau, muka kira shi da ya bayyana a gabanmu kafin karfe 9:00 na safiyar gobe Jumu'a."

"Idan kuma yaki zuwa a wannan lokacin da muka bashi to zamu yi amfani da ƙarfin majalisar ƙasar nan mu ɗauki matakin doka akansa, wanda ya haɗa da bada izinin kamo shi duk inda yake."

KARANTA ANAN: Manyan shugabannin 'yan bindiga 4 sun mika kai a Katsina, sun bada shanu 45 da suka yi fashi

Sanunu ya kara da cewa ba zai yuwu mu zauna mu zuba ido muna ganin mutane na shan wahala saboda yajin aikin likitocin ba, kamar yadda Dailytrust ta ruwaito.

Hakanan muna kira ga likitocin da suka tsunduma yajin aiki da su dubi Allah su saka tausayi a zuƙatansu. Kowa yasan cewa suna da gaskiya a duk buƙatunsu, amma akwai wasu hanyoyi na daban da zasu iya cimma bukatunsu.

Sai dai har yanzun Shugaban MDCN ɗin bai maida martani kan gayyatar da yan majalisun suka sake yi masa ba ranar Jumu'a.

A wani labarin kuma Wata mai juna biyu ta sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu

Yan sanda sun kama wata mata mai ciki kuma uwar 'yaya taƙwas da zargin kashe mijinta a yankin Uwheru dake karamar hukumar Ughelli, jihar Delta.

Matar mai suna Dada ta kashe mijin nata mai suna Jonathan bayan wata yar taƙaddama ta shiga tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel