NSCDC ta kama makiyaya 50 da muggan Makamai a wasu Jihohin ƙasar nan

NSCDC ta kama makiyaya 50 da muggan Makamai a wasu Jihohin ƙasar nan

- Hukumar NSCDC ta bayyana cewa a cikin mako ɗaya ta kama yan ta'adda makiyaya guda 50 a wasu jihohin ƙasar nan

- Kwamandan hukumar na ƙasa, Dr. Ahmed Audi ne ya bayyana haka a yayin miƙa ma wasu jami'ai masu zaman kansu shaidar gudanar da aiki

- Ya kuma ƙara da cewa hukumar sa zata cigaba da gudanar da aikinta yadda ya kamata domin ganin ta sauke nauyin da aka ɗora mata

Jami'an hukumar tsaro ta NSCDC ta damƙe makiyaya yan ta'adda kimanin 50 a cikin makon da ya gabata.

Kwamandan hukumar ta NSCDC na ƙasa, Dr Ahmed Audi,ya bayyana haka a babban birnin tarayya Abuja kamar yadda Punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Yanzu-yanzu: Ƴan bindiga sun sake kai hari ofishin ƴan sanda a Imo, sun sace guda, sun raunta wasu

Ya ƙara da cewa an kama waɗanda ake zargin ne a jihohin Ekiti, Borno, Cross Rivers, da sauransu.

Ya ce ana zargin waɗanda aka kama ɗin da hannu a fashi da makami, satar mutane don neman kuɗin fansa, da kuma satar shanu.

Audi ya faɗi haka ne a yayin da yake bada shaidar gudanar da aiki ga jami'ai 17 masu zaman kansu a ranar Laraba.

NSCDC ta kama makiyaya yan ta'adda 50 da Aikata Manyan Laifuka wasu Jihohin ƙasar nan
NSCDC ta kama makiyaya yan ta'adda 50 da Aikata Manyan Laifuka wasu Jihohin ƙasar nan Hoto: @officialNSCDC
Asali: Twitter

Kwamandan ya kuma ƙara jaddada bukatar dake akwai na haɗin kai tsakanin jami'an tsaro, yana mai cewa za'a magance ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta ne kaɗai idan aka samu haɗin kan da ya kamata a tsakanin jami'an tsaro.

KARANTA ANAN: ‘Dan Majalisar Neja ya kawo kudirin da zai halattawa Musulmai amfani da Hijab a gidan Soja

A jawabin kwamandan NSCDC ɗin ya ce:

"Ƙasar mu na fuskantar matsalar tsaro wanda idan ana son magance ta to dole ne a samu cikakken haɗin kai da aiki tare tsakanin jami'an tsaro da kuma masu faɗa a ji."

"Mun kama makiyaya yan ta'adda guda 50, mun gano wasu daga cikin su na aikata laifin satar shanu, wasu kuma na satar mutane don kuɗin fansa. Mun kama waɗanda ake zargin a sassa daban-daban na ƙasar nan."

Audi ya ƙara da cewa aikin hukumar mu ne muga an sasanta tsakanin makiyaya da manoma, sannan kuma mu bada tsaro ga mutanen da suka zuba jari a fannin noma a ƙasar nan.

Kwamandan na NSCDC ya ce wannan nasarar ta kama mutanen ya nuna yadda jami'an hukumar ke ƙoƙari wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.

Daga ƙarshe Audi ya gargaɗi jami'an masu zaman kansu kan su guji amfani da matsayinsu wajen aikata ayyukan da basu da ce ba.

A wani labarin kuma Jigon PDP ya zargi Gwamna Tambuwal da kokarin tsokano rikici saboda harin takara a 2023

Wani babba a jam’iyyar PDP a jihar Kaduna , Alhaji Adamu Musa Lere, ya na zargin gwamna Aminu Waziri Tambuwal da jawo rigimar cikin-gida.

Adamu Musa Lere ya ce Aminu Tambuwal na neman saba yarjejeniyar da aka tsara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel