Manyan shugabannin 'yan bindiga 4 sun mika kai a Katsina, sun bada shanu 45 da suka yi fashi
- Wasu shugabannin yan fashi hudu sun mika wuya a jihar Katsina
- Maharan da suka mika wuya sun kuma dawo da shanu 45 da suka sata tare da wasu muggan makamai
- An bayyana sunayensu a matsayin Sale Turwa, Mani Turwa, Ado Sarki, da kuma Sani Mai-Daji
Shugabannin 'yan fashin guda hudu a ranar Alhamis, 8 ga watan Afrilu sun mika wuya yayinda suka bayyana cewa sun daina aikata ta’addanci a jihar Katsina.
Har ila yau maharan sun mika shanu 45 da kananan bindigogi biyu, da manyan bindigogin AK 47 24, da alburusai 109 na GMPG da sauran muggan makamai.
Jihar Katsina na daya daga cikin jihohin da ke fama da ayyukan 'yan fashi a duk fadin kasar.
KU KARANTA KUMA: Babbar magana: Buhari bai halarci taron kaddamar da littafin uwar gidansa Aisha ba
A watan Disambar da ta gabata, ’yan fashi sun sace dalibai sama da 300 daga makarantar sakandare na kwana da ke Kankara.
An saki yaran ne mako guda bayan anyi nasarar tattaunawa da masu garkuwar, kamar yadda gwamnatin Katsina ta bayyana.
Sai dai kuma zuwa yanzu ba a sani ba ko an yi wa 'yan fashin da suka mika wuya a ranar Alhamis afuwa, Channels TV ta ruwaito.
Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da batun yin afuwa ga 'yan fashi amma wasu gwamnatocin jihohi, musamman wadanda ke yankin Arewa-maso-Yamma, sun yi na’am da ra'ayin.
An bayyana sunayen shugabannin 'yan fashin su hudu a matsayin Sale Turwa, Mani Turwa, Ado Sarki, da kuma Sani Mai-Daji kuma rahotanni sun ce suna zaune ne a cikin dajin Illela da ke karamar hukumar Safana ta jihar Katsina.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sanusi Buba ya bayyana hakan a wata zantawa da ya yi da manema labarai a hedikwatar rundunar, Katsina.
Buba ya bayyana cewa mika wuyarsu na daga cikin kokarin rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina a ci gaba da kai hare-hare kan yan fashi da makami, masu satar mutane, da sauran nau’ikan laifuka a jihar.
Ya ci gaba da bayanin cewa hakan ya yi daidai da umarnin da Gwamnatin Tarayya ta bayar ga dukkan hukumomin tsaro da su bi ta kan dukkan 'yan fashi a cikin dajin, har sai an kama su, an kashe su, ko kuma tilasta musu mika wuya.
Shugaban 'yan sandan ya ce' yan fashin sun zo ba tare da wani sharadi ba.
KU KARANTA KUMA: 2023: Daga karshe Arewa ta bayyana matsayinta akan zaben shugaban kasa, tayi watsi da tasirin addini
Daya daga cikin tubabbun shugabannin, Ado Sarki ya ce: “Mun zauna mun gano cewa abin da muke yi ba shi da kyau bayan mun sayi manyan makamai don kare shanunmu da kuma kare kanmu.
“Saboda haka mun mika wuya tare da nisanta kanmu daga kungiyoyi daban-daban na‘ yan fashi a dajin. Babu ruwanmu da wadannan makamai. Na yi alkawarin taimakawa hukumomin tsaro a kokarin da muke yi na yakar duk wanda bai shirya tuba ba.”
A wani labarin, wasu 'yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun sace shugaban karamar hukumar Okrika dake jihar Ribas, Honarabul Philemon Kingoli, a Fatakwal.
Wannan lamarin ya faru ne bayan an harbe tare da kashe wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan kungiyar asiri ne a wani otal dake Fatakwal.
Leadership ta tattaro cewa, Kingoli wanda cikin kwanakin nan ya rasa damar hayewa kujerarsa a karo na biyu karkashin jam'iyyar PDP, an sace shi ne a kan titin Peter Odili dake Fatakwal.
Asali: Legit.ng