Wata mai juna biyu ta sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu

Wata mai juna biyu ta sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu

- Wata mata mai ciki ta kashe mijinta har lahira bayan wata yar taƙaddama ta shiga tsakaninsu wadda takai su har ga faɗa

- Matar dake da 'yaya takwas ta saba dawowa gida daga wajen aiki a makare, wanda hakan na ɓatawa mijin rai har takai ga ya gargaɗi matar tasa da ta bari.

- Shaidun gani da ido sun bayyana cewa a ranar da abun ya faru matar ta sake dawowa gida a makare, sai mijin ya ƙalubalanceta akan karya dokarsa, wanda hakan yasa ta caka mishi wuƙa

Yan sanda sun kama wata mata mai ciki kuma uwar 'yaya taƙwas da zargin kashe mijinta a yankin Uwheru dake karamar hukumar Ughelli, jihar Delta.

Matar mai suna Dada ta kashe mijin nata mai suna Jonathan bayan wata yar taƙaddama ta shiga tsakaninsu.

KARANTA ANAN: Ku bada himma wurin samar da tsaro a maimakon zawarcin mu, Gwamnonin PDP ga APC

Rahoton jaridar Punch ya bayyana cewa matar ta dawo daga wajen aiki a makare a ranar 5 ga watan Afrilu, 2021 lokacin da taƙaddama ta ɓarke tsakninta da mijinta.

Sai dai taƙaddamar ta su ta ɗau zafi har takai ga sun fara faɗa tsakaninsu, wanda hakan yasa matar ta ɗauki wuƙa ta caka wa mijinta.

Wani shaidar gani da ido da ya nemi a sakaya sunansa yace mutumin da aka kashe ɗin ya gargaɗi matar tasa kan yawan dawowa a makare da take yi daga wurin aiki.

Wata Mata Mai Ciki ta Sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a Tsakaninsu
Wata Mata Mai Ciki ta Sheƙe mijinta har Lahira bayan taƙaddama ta ɓarke a Tsakaninsu Hoto: @MobilePunch
Source: Twitter

Shaidar ya ƙara da cewa, daman matar ta saba dawowa a makare amma mijin nata ya gargaɗe ta da ta bari.

KARANTA ANAN: Ta tabbata: Rigakafin Astrazeneca na haddasa daskarewar jini musamman jikin matasa, Hukumomin Turai

A ranar da lamarin ya faru matar ta dawo a makare kamar yadda ta saba sai mijin ya ƙalubalance ta a kan karya masa dokokinsa.

Ya cigaba da cewa, nan da nan sai taƙaddama ta ɓarke a tsakaninsu, matar ta ɗakko wuƙa ta dinga caka wa mijin nata har saida ta kashe shi.

Lokacin da aka tuntuɓi mai magana da yawun yan sandan jihar na riƙon kwarya, Edafe Bright, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce hukumar yan sanda tasan da faruwar lamarin, kuma jami'an mu dake ofishin Ughelli sun kama matar. Ya ƙara da cewa a yanzun haka an mikawa hukumar bincike ta jihar (CID) lamarin.

A wani labarin kuma Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Ministan aikin noma da raya karkakara, Sabo Nanono ya auri wata yarinya mai shekaru 18 a wani ɗaurin auren da aka yi cikin sirri.

Majiya daga iyalan ministan ta tabbatar da daurin auren inda tuni matar ta tare a gidan ministan a Kano.

Source: Legit.ng

Online view pixel