Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18

- Ministan Noma da raya karkara, Sabo Nanono ya yi auri wata budurwa mai shekaru 18 daga Kaduna

- Majiya daga iyalan ministan ta tabbatar da daurin auren inda tuni matar ta tare a gidan ministan a Kano

- Majiyar ta kuma ce iyalan ministan ba su so auren ba duba da banbancin shekaru 50 ke tsakanin ministan da amaryar amma hakan bai hana shi ba

Ministan aikin noma da raya karkakara, Sabo Nanono ya auri wata yarinya mai shekaru 18 a wani ɗaurin auren da aka yi cikin sirri kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Mr Nanono, mai shekaru 74 ya auri kyakkyawar yarinyar a auren sirri da mutum uku daga danginsa kadai suka hallarci ɗaurin auren da aka yi a Jere a jihar Kaduna.

Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18
Ministan Buhari mai shekaru 74 ya yi wuff da budurwa mai shekaru 18. Hoto: @daily_nigerian
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun bi dare sun sace shugaban kwamitin riƙo jam'iyyar APC a gidansa

"Mutane uku kawai ministan ya wakilta kuma ya gargaɗe su da kada su bayyana wa mutane cewa ya yi aure," a cewar wani majiya daga iyalin da ya nemi a boye sunansa.

Daily Nigerian ta gano cewa tuni amaryar ta tare a gidan Ministan da ke Tarmandu Close a Kano.

Duk da cewa iyalan ministan ba su ya auri yarinyar da ya girma da shekaru 50 ba, majiyoyi sun ce ya tsaya kan bakansa sai da aka yi auren.

"Ministan ya tsunduma kogin soyayya. Bisa dukkan alamu babu abin da zai sauya masa ra'ayi," a cewar majiyar.

KU KARANTA: Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

A watan Oktoban 2019, ministan ya ce babu yunwa a Nigeria tunda akwai abinci na N30.

"Abinci na araha a Nigeria idan aka kwatanta da sauran ƙasashe. Misali, a Kano zaka iya cin abincin N30 ka ƙoshi. Don haka mu gode Allah cewar abinci da sauƙi kuma muna iya ciyar da kanmu," in ji shi.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Source: Legit

Online view pixel