'Yan bindiga sun bi dare sun sace shugaban kwamitin riƙon jam'iyyar APC a gidansa

'Yan bindiga sun bi dare sun sace shugaban kwamitin riƙon jam'iyyar APC a gidansa

- Masu garkuwa da mutane sun sace shugaban kwamitin riko na jam'iyyar APC a jihar Rivers

- An sace Hyacinth Nwiye ne a ranar Lahadi da daddare a gidansa da ke karamar hukumar Khana kamar yadda PM News ta ruwaito

- Jam'iyyar ta All Progressives Congress ta yi Allah-wadai da sace shugabanta da masu garkuwa suka yi

Wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace Hyacinth Nwiye, shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a karamar hukumar Khana a jihar Rivers.

Kakakin jam'iyyar, Ogbonna Nwuke, ya bayyana cewa an sace Nwiye ne a daren ranar Lahadi 4 ga watan Afrilu a gidansa da ke Khana kamar yadda PM News ta ruwaito.

'Yan bindiga sun sace mukadashin shugaban jam'iyyar APC a gidansa
'Yan bindiga sun sace mukadashin shugaban jam'iyyar APC a gidansa. Hoto: @TheNationNews
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

Nwuke ya ce: "Wasu mutane da ba mu san ko su wanene ba sun sace shugaban kwamitin rikon kwarya na APC a karamar hukumar Khana a jihar Rivers a gidansa, ranar Lahadi.

"An sanar da mu cewa an sace shi ne a lokacin da sauran mutanen kirki ke murnar bikin Easter na almasihu."

Jam'iyyar ta bukaci a sako mata jigon ta ba tare da wani bata lokaci ba.

A cewar The Nation, APC ta ce gwamnatin jihar Rivers ne ke da laifi domin ta gaza bawa mutane musamman talakawa kariya da ya dace.

KU KARANTA: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Jam'iyyar ta yi kira ga jami'an tsaro su yi duk mai yiwuwa domin ganin sun ceto danta da aka sace.

A bangare guda kun ji cewa gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a ragu.

Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.

Source: Legit

Tags:
Online view pixel