Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sandan da ya shiga yi wa sata

- An kama wani matashi mai shekaru 22 da ya kutsa ya shiga gidan dan sanda domin yin sata

- Barawon ya yanke shawarar ya kwanta ya huta na mintuna biyar ne amma barcin ya zarce

- Yan sanda sun kama barawon duk da bai fara satar ba kuma za a gurfanar da shi saboda kutse da balle gida

Wani barawo ya bige da barci a cikin gidan da ya shiga yin sata, daga bisani jami'an yan sanda sun tashe shi daga barcin. Ashe gidan dan sanda ne ya shiga yin satar.

Lamarin ya faru ne a ranar 22 ga watan Maris na yankin Nam Rorn da ke Wichianburi a Petchabun a arewa maso gabashin kasar Thailand.

Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sanda da ya shiga yin sata
Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sanda da ya shiga yin sata. Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sanda da ya shiga yin sata
Hotunan ɓarawon da aka kama yana sharɓar barci a gidan ɗan sanda da ya shiga yin sata. Hoto: @TheNationNews
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda

Saja Sakda Jiamprasert ya farka tsakar dare misalin karfe 2 ya ji karar na'urar sanyaya daki wato AC a dakin yarsa.

Duba da cewa ya san yarsa ta yi tafiya na wasu yan kwanaki, dan sandan ya fita waje ya leka dakin ta taga.

Nan ne fa ya hangi barawon, Athip Kinkhunthot yana sharbar barci a gadon yarsa sannan ga kayan da ya yi amfani da su wurin balle kofar gidan a gefe.

Nan take Sakda ya kira karin yan sanda domin su taimaka masa.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock

Kinkhunthot mai shekaru 22 ya yi barci mai nauyi har ma yana ta magagin barci a lokacin da yan sandan suka tashe shi daga barcin.

A cewar kafar watsa labarai na Thailand, The Nation, barawon ya shaidawa yan sanda cewa ya dade yana neman inda zai shiga ya yi sata a unguwar kuma ya gaji sosai.

Ya kutsa gidan Jami'in Dan sanda Jiamprasert amma sai ya yanke shawarar ya dan kwanta ya huta kafin ya saci abin da zai samu a gidan.

Kinkhunthot ya kunna na'urar AC din ne domin ya yi barcin mintuna biyar amma ya zarce kwatsam kuma sai ya ji yan sanda sun tashe shi.

Duk da cewa bai sata komai ba, an kama shi saboda kutse da lalata kaya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel