Ganduje ya zabtare rabin albashinsa da na sauran masu riƙe da muƙaman siyasa
- Abdullahi Umar Ganduje, gwamnan jihar Kano ya rage wa dukkan masu rike da mukaman siyasa albashi a watan Maris
- Gwamnatin jihar Kano ta ce an dauki wannan matakin ne saboda kudaden da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya a duk wata ya ragu
- Mohammed Garba, kwamishinan watsa labarai na jihar ya ce wannan ragin albashin ya shafi gwamna, mataimakinsa, ciyamomi da sauransu
Gwamnatin Jihar Kano ta rage albashin masu rike da mukaman siyasa a jihar da kashi 50 cikin 10 na watan Maris saboda karancin kudade, Vanguard ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Allah ya yi wa direban Buhari rasuwa a asibitin Aso Rock
Kwamishinan labarai na jihar, Muhammad Garba, ne ya bayyana wa manema labarai hakan a ranar Talata inda ya ce hakan ya faru ne saboda kudin da jihar ke samu daga gwamnatin tarayya ya ragu.
Kwamishinan ya ce matakin ta shafi gwamna, mataimakinsa da dukkan masu rike da mukaman siyasa a jihar da suka hada da kwamishinoni, masu bada shawara na musamman, manyan masu taimakawa da masu taimakawa na musamman da sauransu.
KU KARANTA: Usman Alkali Baba: Abubuwa 6 da ya kamata ku sani game da sabon Babban Sufetan 'Yan Sanda
Garba ya ce a kananan hukumomin, ragin albashin ya shafi shugabannin kananan hukumomi, mataimakansu, zababbun kansiloli, mukadashin kansila, masu bada shawara da sakatarorin kananan hukumomi.
A wani rahoton daban, Fadar Shugaban Kasa a ranar Lahadi ta ce kalaman Bishop din Katolika na Jihar Sokoto, Mathew Kukah, basu yi kama da na malamin addini ba a sakon sa na bikin Easter inda ya soki shugaban kasa, Muhammadu Buhari da gwamnatinsa.
Babban mai taimakawa shugaban kasa bangaren yada labarai, Garba Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa mai taken "kalaman Kukah kan Buhari rashin adalci ne," The Punch ta ruwaito.
Shehu ya ce tunda dai Kukah ya ce shi malami ne, bai kamata ya dauki bangaranci wajen yin adalci da fadar gaskiya ba.
Asali: Legit.ng