Labari Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Kansila a Kaduna

Labari Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Kansila a Kaduna

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe, Dayyabu Jafar, tsohon kansila a jihar Kaduna

- Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin

- Aruwan ya ce tsohon kansilar na aiki a gonarsa da ke Unguwan Fadama ne yan bindigan suka afka masa suka kashe shi

'Yan bindiga sun kashe, Dayyabu Jafar, tsohon kansila a mazabar Gayam da ke karamar hukumar Birnin Gwari a jihar Kaduna.

A cewar rahoton TVC News, yan bindigan sun kai masa hari ne yayin da ya ke aiki a gonarsa da ke Unguwan Fada.

DUBA WANNAN: Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

Labari Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Kansila a Kaduna
Labari Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Kashe Tsohon Kansila a Kaduna. Hoto: @TVCNews
Source: Twitter

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar ya tabbatar da afkuwar lamarin a ranar Alhamis.

A cewarsa, yan bindigan sun kashe tsohon kansilar ne yayin da ya ke aiki ne a gonarsa da ke Unguwan Fada a jihar.

KU KARANTA: NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

Aruwan ya kuma ce a wani harin na daban, yan bindiga sun halaka wani mutum, Yusuf Dallatu, a kasuwan Magani a karamar hukumar Kajuru a jihar ta Kaduna.

"Jami'an tsaro sun ruwaito cewa yan bindiga sun kashe tsohon kansilar mazabar Gayam a karamar hukumar Birnin Gwari," in ji Aruwan.

Aruwan ya ce an fara bincike a kan lamarin inda ya bawa mutanen jihar tabbacin cewa gwamnan jihar Nasiru El-Rufai yana yin dukkan mai yiwuwa domin ganin an kawo karshen kallubalen tsaro da ke adabar jihar.

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Source: Legit

Online view pixel