NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano

- Hukumar Kula Da Igancin Magunguna da Abinci, NAFDAC, ta gano abinda yayi sanadin bullar bakuwar cuta a Kano

- NAFDAC ta ce gwajin da ta yi ya nuna cewa wani sanidarin mai guba ne da ake sayar da shi da suna 'citric acid' ko 'Dan Sanmi'

- Hukumar tace ta haramtacciyar hanya aka shigo da sinadarin da aka rika siyarwa a kasuwanni ana amfani da shi wurin hada abin sha

Makonni biyu bayan bullar wata sabuwar cuta a birnin Kano, Hukumar Kula Da Igancin Magunguna da Abinci, NAFDAC, ta gano abinda ya haifar da cuta a Kano, rahoton The Punch.

A cewar hukumar, wani sinadarin kemikal mai hatsari ne ake siyar da shi da sunan citric acid, wanda ake kira Dan Sanmi, shine ya haifar da cutar wadda ta yi sanadin salwantar rayyuka hudu ya kuma kwantar da mutum fiye da 300 a asbiti.

NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano
NAFDAC Ta Gano Abinda Ya Janyo Cutar Da Ta Kashe Mutum 4, Ta Kwantar Da 400 a Kano. Hoto: @MobilePunch
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

Shugaban NAFDAC na kasa, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta bada wannan tabbacin a ranar Talata a Kano, jim kadan bayan ta gana da gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje a gidan gwamnati a Kano.

Farfesa Adeyeye, ta yi ikirarin cewa an shigo da sinadarin ne cikin Nigeria ta wani hanya da ba a gano ba aka sayarwa yan kasuwa kan N3000 a maimakon N30,000 wanda shine ainihin farashinsa.

"Kafin yanzu, ana amfani da sinadarin na Dansanmi domin samun dandanon tsami a abubuwan sha, amma a wannan karon guba aka yi amfani da shi a madadin sinadarin da ya yi sanadin rasuwar mutum uku da kuma wasu da suka kwanta jinya.

KU KARANTA: 2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC

"Uku cikin abubuwan shan ba su da rajista da NAFDAC, biyu kadai ke da rajista. Abinda ya kamata a siya N30,000 an zo ana sayar da shi N3,000, yayinda wasu na siyar da shi N10,000."

Adeyeye ta yi alkawarin cewa za a gabatar da sahihin rahoto kan sakamakon gwaje-gwajen da aka yi da zarar an kammala bincike.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel