Mahaifi Ya Kashe Ɗansa Ta Hanyar Lakaɗa Masa Duka a Kano

Mahaifi Ya Kashe Ɗansa Ta Hanyar Lakaɗa Masa Duka a Kano

- Yan sanda a Kano sun tabbatar da kama uban da ya kashe ɗansa ta hanyar lakada masa duka saboda zarginsa da sata

- Yan sandan sun ce an tsare mahaifin an tura shi sashin binciken manyan laifuka bangaren kisan kai ana bincike

- Mahaifiyar yaron, wadda ta dade da rabuwa da mahaifin ta bayyana yadda yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali

- Wasu da abin ya faru a kan idonsu sun bayyana yadda wani ya yi yunkurin hana mahaifin dukan yaron amma bai yi nasara ba

Rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Mahaifi Ya Halaka Ɗansa Ta Hanyar Lakaɗa Masa Duka a Kano
Mahaifi Ya Halaka Ɗansa Ta Hanyar Lakaɗa Masa Duka a Kano. Hoto: @Vanguardngrnews
Source: Twitter

DUBA WANNAN: 2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC

Mahaifin ya yi wa dansa duka ne kan zarginsa da sace masa kaya a shago

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

"Muna zaune a cikin shago a nan wurin sai muka ji yana dukan yaronsa a cikin shago, sunan shi Auwalu amma an fi saninsa da Abba, mun tsaya a waje a nan wurin yana ta dukan yaron badai wanda ya je wurin sai makwabcinsa mai wankin hula, ya zo ya same shi, ya ce mishi ... ya dai masa magana, ni banji abinda ya fada masa ba, amma na ji lokacin da shi mahaifin ya ke masa tsawa ya ke ce masa ya fita masa a shago, ganin haka yasa muma ba mu tafi wurin ba," a cewar Kabiru

KU KARANTA: An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

Hajiya Goshi Muhammad, mahaifiyar yaron wadda ta dade da rabuwa da mahaifin tsawon lokaci ta ce yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali ta tambaye shi abinda yafaru, sai ya fada cewa mahaifinsa ne ya doke shi saboda wai bai ga 'mansa ba guda biyu'.

Yaron ya shaidawa mahaifiyarsa cewa mahaifinsa ya yi ta dukansa a kai da ciki duk da cewa ya fada masa ba shine ya sace kaya a shagon ba.

Rundunar yan sandan Kano ta bakin kakakinta ya ce mahaifin yaron yana hannunsu,an mika shi sashin binciken manyan laifuka, bangaren kisar kai ana cigaba da bincike a kansa.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Source: Legit.ng

Online view pixel