Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su

- Wasa matasa biyu a jihar Bauchi sun 'gane kurensu' bayan yi wa gwamna Bala Mohammed ihun 'Ba mayi'

- Lamarin ya faru ne a garin Azare a yayin da gwamnan ya tafi duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ta bada kwangila

- Jami'an tsaro da ke tawagar gwamnan sun damke matasan biyu sun suburbude su sannan suka jefa su cikin motar yan sanda

Wani abu mai kama da dirama ya faru a karamar hukumar Azare ta jihar Bauchi a lokacin da wasu matasa biyu da ba a bayyana sunansu ba suka yi wa Gwamna Bala Mohammed ihu cikin fushi.

Gwamnan ya tafi duba wasu ayyuka da gwamnatinsa ta bada ne a sassan jihar a Cibiyar Lafiya Birane na Azare a ranar Alhamis a yayinda abin ya faru.

Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su
Wasu Matasa Sun Yi Wa Gwamnan Bauchi Ihun 'Ba Ma Yi' a Gabansa, Jami'an Tsaro Sun Suburbuɗe Su. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUB WANNAN: Gobara: Badaru, Bagudu da Barkiya Sun Gwangwaje Ƴan Kasuwan Katsina Da Miliyoyin Naira

Wakilin The Nation da ke cikin tawagar gwamnan ya ruwaito cewa matasan biyu duk da akwai jami'an tsaro a wurin sun rika ihu suna cewa 'Ba ma yi!' ma'ana ba su goyon bayan gwamnan.

Duk da cewa Gwamna Mohammed bai kula su ba, jami'an tsaro da ke tawagarsa sun kama matasan biyu.

Jami'an tsaron sun bi su da gudu bayan sun kama su suka sharara musu mari sannan suka jefa su cikin motar yan sanda.

Wani jami'in rundunar yan sanda ta RRS a jihar Bauchi, wanda ya nemi a boye sunansa ya shaidawa majiyar Legit.ng cewa abinda matasan suka yi rashin girmama na gaba ne.

KU KARANTA: Bidiyo Da Hotunan Wani Ɗan Chadi Da Aka Kama Yana Sayarwa Boko Haram Miyagun Ƙwayoyi

"Ka duba fa, ta yaya za ka fadawa gwamna gaba da gaba cewa baka son sa kuma baka goyon bayan gwamnatinsa, cin mutunci ne."

Amma ba a tabbatar ko an saki matasan ba a lokacin hada wannan rahoton.

A wani labarin daban, rundunar yan sanda a jihar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma'a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Acewar wani da al'amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa

Asali: Legit.ng

Online view pixel