An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

- 'Yan daba sun sake halaka wani sufetan dan sanda a garin Ikot Afanga a jihar Akwa Ibom

- 'Yan daban sun tafi gidan dan sandan ne cikin dare suka banka wuta yana barci

- Rundunar yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar lamarin ta kuma fara bincike da nufin kama miyagun

Hankulan mutane sun tashi a garin Ikot Afunga a karamar hukumar Essien Udim a jihar Akwa Ibom a jiya Litinin a yayin da yan daba suka sake cinnawa wani dan sanda mai mukamin sufeta wuta a gidansa.

An gano cewa yan daban sun afka gidan dan sandan mai suna Aniekan misalin karfe 2.30 na dare suka zagaye gidan suka cinna wuta a lokacin yana barci, Vanguard ta ruwaito.

DUBA WANNAN: Hotunan Zulum Ya Tsayar Da Ayarin Motocinsa Ya Ɗauki Mata Da Suka Ɗebo Itace Daga Daji

An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom
An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

Wannan shine karo na uku da yan daba ke kai wa yan sanda hari a gida da caji ofis a karamar hukumar.

Idan za a iya tunawa a ranar 22 ga watan Fabrairun 2021, yan daba sun kai hari a Ikpe Annang Junction, sun kone dan sanda da ransa a cikin motar sintiri yayin da saura suka gudu.

Wani mazaunin unguwar da ya nemi a boye sunansa yace kisar ba zai rasa nasaba da rawar da dan sandan ya taka ba wurin tsare masu laifi da gurfanar da su a kotu.

KU KARANTA: Da Ɗumi-Ɗumi: Ƴan Daba Sun Kaiwa Hadimin Ministan Buhari Da Wasu Ƴan Majalisa Hari a Osun

Kakakin rundunar yan sandan jihar Mr Odiko MacDon ya tabbatar da afkuwar inda ya ce abin bakin ciki ne kuma ana bincike.

"Kwamishinan yan sandan jihar, Mr Andrew Amiengheme ya nuna bakin cikinsa kan afkuwar lamarin ya kuma yi wa iyalan mamacin ta'aziya.

Ya bada umurnin yan sanda su bazama bincike a garin. Ana cigaba da bincike a yanzu kuma ya bada tabbacin za a kamo wadanda ke da hannu a hukunta su.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel