Yanzu-Yanzu: Shugaban PDP da Manyan Ƴan Jam'iyyar Sun Dunguma Sun Koma APC a Ebonyi
- Onyekachi Nwebonyi, shugaban jam'iyyar PDP a jihar Ebonyi ya koma APC
- Suma sauran shugabannin jam'iyyar sun dunguma sun sauya sheka zuwa APC
- Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki
Shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.
Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.
DUBA WANNAN: Da Ɗuminsa: Rundunar Soji Ta Fitar Da Sunayen Mutum 300 Waɗanda Suka Yi Nasara Da Ranar Tantancewa
Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.
Idan za a iya tunawa, shugabannin jam'iyyar PDP na kasa a karshen shekarar 2020 sun kori Nwebonyi daga jam'iyyar bayan gwamnan jihar ya koma APC.
KU KARANTA: Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu
Amma shi da sauran shugabannin jam'iyyar a jihar sun tafi kotu domin kallubalantar korarsu.
A watan Fabrairu, babban kotu da ke zamanta a Abakaliki sun soke korar da aka musu sun kuma rushe kwamitin riko ta Fred Udogu da shugabannin jam'iyyar suka naɗa.
Kwamitin na Udogu ta tafi kotu domin ɗaukaka kara kan rushe ta kuma kawo yanzu kotu bata yanke hukuncin kan batun ba.
A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.
Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters
Asali: Legit.ng