2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC

2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC

- Onyekachi Nwebonyi, tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Ebonyi ya ce ya yi farin cikin komawa APC

- Nwebonyi, ya ce rashin adalci da ake yi wa Ibo da wasu dalilan ne suka saka shi ya fice daga jam'iyyar

- Tsohon shugaban na PDP ya ce Ibo sun bada gudunmawa sosai wurin gina PDP amma da lokacin basu damar takarar shugaban kasa ya yi sai aka hana su

Tsohon shugaban jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, a jihar Ebonyi, Onyekachi Nwebonyi ya ce ya yi farin cikin ficewa daga jam'iyyar, inda ya ce rashin adalci na daga cikin dalilin da yasa ya fice, rahoton Vanguard.

Nwebonyi, yayin bikin tarbarsa da aka yi a Abakaliki bayan gwamnan jihar David Umahi ya nada shi a matsayin kwamishinan babban birnin jihar Abakaliki, ya kara da cewa rashin bawa yankin kudu takarar 2023 alama ce da ke nuna suna nunawa Ibo bangaranci.

2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC
2023: Tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Ya Ce Ya Yi Farin Cikin Komawa APC. Hoto: @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: An Sake Cinnawa Sufetan 'Yan Sanda Wuta Da Ransa a Akwa Ibom

"Na yi farin cikin barin PDP saboda cike take da rashin adalci. Kana iya ganin jam'iyyar bata yi wa ibo adalci.

"Ka tuna, Ibo ne suka bada gudunmawa kashi 70% wurin kafa PDP a 1998, mun yi wa jam'iyyar hidima sosai.

"Muna taka rawar da ya kamata mu yi a jam'iyyar wurin zabe amma da lokacin mu ya yi a 2023 sai jam'iyyar ta ce babu tikiti.

"Me yasa sai da lokacin ibo ya zo sannan za ku ce kowa na iya takarar, lokacin kudu maso yamma, kun basu, lokacin arewa, kun basu.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: Bidiyon Yadda Aka Tarbi Buhari a Birnin Landan

"Yanzu da lokacin kudu maso gabas ya yi, kuma kuna cewa ba za a cigaba da karba-karba ba, wannan ai yaudara ne," in ji shi.

Tsohon shugaban na PDP ya yi wa gwamnan godiya saboda bashi mukamin kwamishina na babban birnin jihar wato Abakaliki.

A wani rahoton daban, kun ji shugaban jam'iyyar People's Democratic Party, PDP, na jihar Ebonyi, Barista Onyekachi Nwebonyi da kwamitin shugabannin jam'iyyar, a ranar Asabar, sun koma jam'iyyar All Progressives Congress, APC, a jihar.

Sauran da suka sauya sheka zuwa APC sun hada da shugabannin ƙananan hukumomi 13 da shugabannin gundumomi 171 na jam'iyyar, The Nation ta ruwaito.

Anyi bikin sauya sheƙan ne a filin wasanni na Pa Oruta da ke Abakaliki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel