Kano: Dole 'yan siyasa su nuna shaidar biyan Zakka kafin su tsaya takara
- Daraktan hukumar Zakka ta jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace jihar na shirin mayar da Zakka dole ga masu damar biya
- Kamar yadda Abubakar ya sanar, daga yanzu duk wanda ke neman kujerar siyasa, sai ya nuna shaidar biyan Zakka
- Ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin rantsar da kwamitin Zakka a ofishinsa
Darakta janar na hukumar Zakkah da Hisbah na jihar Kano, Safiyanu Abubakar, yace ana shirin mayar da biyan Zakka ya zama wajibi ga dukkan 'yan siyasa kafin su tsaya takara a jihar.
Abubakar ya sanar da hakan a ranar Alhamis a ofishinsa yayin rantsar da kwamitin mutum 11 na karbar Zakka a jihar.
Kamar yadda yace, wannan al'amarin ana son tabbatar dashi ne domin taimakon mabukata a jihar.
KU KARANTA: Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje
KU KARANTA: Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi
"Ya zama dole ga kowannen mai hali ko kungiya da su fitar da wani kaso na dukiyarsu a matsayin Zakka," yace.
Abubakar ya kara da yin bayanin cewa hukumar ta zo da wannan sabon salon ne ta yadda kowanne mai hannu da shuni zai biya zakka,
"'Yan majalisun jihar, ballantana na kwamitin lamurran addinin sun zauna tare da tattaunawa a kan muhimmancin Zakka.
“A matsayinmu na kwamitin, muna kokarin kaiwa matsaya ta yadda duk mai neman wata kujera a jihar sai ya bada shaidar yana biyan Zakka ga hukumar," yace.
A wani labari na daban, dakarun rundunar Operation Thunder Strike da na Div 1 dake Kaduna sun ragargaza maboyar 'yan bindiga dake yankin Buruku a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.
Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.
Kamar yadda kwamishinan ya sanar, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne har mutum biyu sun sheka lahira yayin samamen.
Asali: Legit.ng