Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna

- Sojojin rundunar Operation Thunder Strike tare da na Div 1 sun kai samamen maboyar 'yan bindiga a Chikun

- Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, yace 'yan bindiga 2 sun sheka lahira

- Kamar yadda ya bayyana, wasu 'yan bindigan sun tsere da miyagun raunika daga sansaninsu dake Buruku

Dakarun rundunar Operation Thunder Strike da na Div 1 dake Kaduna sun ragargaza maboyar 'yan bindiga dake yankin Buruku a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna.

Samuel Aruwan, kwamishinan tsaron cikin gida na jihar, ya tabbatar da aukuwar lamarin a wata takarda da ya fitar a ranar Laraba.

Kamar yadda kwamishinan ya sanar, wasu da ake zargin 'yan bindiga ne har mutum biyu sun sheka lahira yayin samamen.

Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, ya kara da cewa ayyukan rundunar sojin ya shafi kananan hukumomi hudu na jihar Kaduna.

KU KARANTA: Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna
Sojoji sun sheke 'yan bindiga 2 yayin da suka kai samame maboyarsu a Kaduna. Hoto daga @Thecableng
Asali: UGC

KU KARANTA: Kyawawan hotunan sarakuna 3 masu karancin shekaru a Najeriya da cikakken tarihinsu

"'Yan bindiga masu tarin yawa sun tsere da miyagun raunika yayin samamen da ya shafi kananan hukumomi biyar na yankin Kaduna ta tsakiya," takardar tace.

"Rundunar sojin ta bayyana wannan cigaban da take samu ga gwamnatin jihar Kaduna.

“Kamar yadda rahoton ya nuna, rundunar ta fara aikin bincike tare da tseratarwa a dajin Buruku, kauyen Rima dake karamar hukumar Chikun."

Aruwan ya kara da cewa, Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, ya mika godiyarsa ga dakarun sojin tare da jinjina musu a kan nasarar da suka samu.

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Jigawa kuma shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar APC, Badaru Abubakar, yace za a yi gagarumin taron jami'iyyar a watan Yuni.

Daily Trust ta ruwaito cewa, akwai rade-radin dake yawo na cewa za a kara wa'adin mulkin Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe a matsayin shugaban kwamitin tsari na jam'iyyar kuma za a kara lokacin taron ya wuce watan Yuni.

Amma a wata tattaunawa da manema labarai a sakateriyar jam'iyyar APC da yayi a ranar Talata, Badaru yace kwamitin rikon kwaryan ya shirya domin sauke nauyin dake kansu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel