Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje

Tsarikan makiyaya da kake fadi ba kamar kalmashe daloli bane, Miyetti Allah ga Ganduje

- Sakataren kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, Saleh Alhassan, yace wasu 'yan bindiga makiyaya ne da suka rasa shanunsu

- Alhassan ya zargi wasu gwamnonin da janyo al'amuran 'yan bindiga da kansu saboda hana kiwo da suka yi a jihohinsu

- Ya caccaki Ganduje da kiran makiyaya da yayi arewa, inda yace tsarikan da yake bayyanawa ba kamar kalmashe daloli bane a babbar riga

Saleh Alhassan, sakataren kasa na kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore, yace wasu 'yan bindigan makiyayya ne da suka zama tsageru sakamakon rasa shanunsu da suka yi saboda wasu gwamnoni sun hana kiwo.

Ya sanar da hakan ne a wata tattaunawa da yayi da Punch a ranar Laraba.

Alhassan ya caccaki Abdullahi Ganduje, gwamnan jihar Kano, a kan matsayarsa na cewa makiyaya su dawo arewa kacokan.

A watan Janairu ne Ganduje yace ya kamata a saka dokar da za ta haramta kaiwa da kawowar shanu daga arewa zuwa kudu.

KU KARANTA: Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

Miyetti Allah: Wasu 'yan bindigan makiyaya ne da suka rasa shanunsu
Miyetti Allah: Wasu 'yan bindigan makiyaya ne da suka rasa shanunsu. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: APC zata yi gagarumin taron jam'iyya na kasa a watan Yuni, Badaru

Amma a wata tattaunawa, Alhassan ya kwatanta zantukan gwamnan da zantukan siyasa matukar bai ajiye abinda makiyayan ke bukata ba amma yake gayyatarsu jiharsa.

Ya kara da cewa, wannan tsarin kuwa ba mai sauki bane kamar "adana daloli" a aljihun mutum ba.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun halaka wasu mutum hudu da suka hada da ma'aikacin lafiya daya a kananan hukumomin Igabi da Jema'a na jihar Kaduna a ranar Litinin, sun bar wasu da raunika daga harsashi.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, lamarin ya faru a kauyen Unguwan Lalle dake karamar hukumar Igabi da asibitin Niima dake kauyen Golgofa a karamar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna, jami'an gwamnatin jihar suka tabbatar.

A wata takarda da kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan, ya fitar, ya sanar da cewa tun farko 'yan bindigan sun yi yunkurin rufe titin Kwanar Tsintsiya dake babbar hanyar Kaduna zuwan Abuja, amma sojoji suka fattatakesu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng