Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi

Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi

- Nelius Wangui Mainawas 'yar kasar Kenya ce da aka gurfanar a gaban kotu sakamakon satar wayar saurayi

- Maina tace ta sace wayoyi biyu na saurayinta ne bayan ta kai masa ziyara amma ya ki bata kudin motan komawa gida

- Bayan ziyarar da ta kai masa, ya shiga wanka inda tayi saurin dauke wayoyinsa masu darajar Sh37,500 da Sh40,300

Wata 'yar kasar Kenya, Nelius Wangui Mainawas ta gurfana a gaban wata kotu sakamakon zarginta da ake da sace wayoyi biyu daga wurin wani mutum da tace saurayinta ne.

An gurfanar da Maina a gaban wata kotun Makadara a ranar Talata, 23 ga watan Maris, a kan satar wayoyi biyu na Eric Basweti amma tace mai korafin saurayinta ne.

Ta yi korafin cewa ta sace wayoyin ne saboda ta rike su har sai ya biyata kudin motan da ya hana ta.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kutsa jihar Kaduna, sun sheke ma'aikacin lafiya da wasu mutum 3

Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi
Ziyara na kai masa amma ya hana ni kudin mota, budurwar da ta sace wayoyin saurayi.Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwara: Rikici kan hijabi ya haɓaka, ƴan daba sun kai hari makarantu da kantuna

Kamar yadda Maina ta sanar, ta je wurinsa tun daga Nakuru har Basweti dake Nairobi amma ya hana ta kudin motan komawa gida.

An gano cewa Maina ta sace wayoyinsa biyu masu darajar Sh37,500 da Sh40,300 a gidansa dake South B estate a yankin Makadara a ranar 18 ga watan Maris.

Wanda ke korafin ya shiga bandaki yayin da wacce ake zargin ta dauka masa wayoyi kuma daga baya ta tura Sh40,300 daga M-PESA dinsa zuwa wasu wayoyi.

Maina ta shiga hannu ne bayan mai abun hawan haya da ya dauketa ya sanar da 'yan sanda kuma aka tuntubi Basweti, The Nation ta wallafa.

Ta amsa laifinta a gaban Alkali Angelo Kithinji kuma an saketa a kan belin Sh50,000.

Za a cigaba da sauraren shari'ar zuwa ranar 6 ga watan Afirilun 2021.

A wani labari na daban, 'yan bindiga sun sheke 'yan sanda uku a sabon harin da suka kai karamar hukumar Ohafia ta jihar Abia.

The Cable ta gano cewa 'yan sanda da aka kashe a safiyar Litinin suna kan titi ne yayin da suke duba motoci masu wucewa.

An gano cewa 'yan sandan sun kai harin sannan suka yi awon gaba da bindigogin jami'an tsaron. 'Yan sandan da aka kashe sun hada da: Austin Ugwu, Longinus Ugochukwu da Ama Ifeanyi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel