Matsalar Tsaro: Gwamnan Rivers ya ba Shugaban Sojoji wata Muhimmiyar shawara

Matsalar Tsaro: Gwamnan Rivers ya ba Shugaban Sojoji wata Muhimmiyar shawara

- Gwamnan jihar Rivers, Nyesom Wike, ya bama shugaban sojin ƙasar nan shawara kan ya raba sojoji da 'yan siyasa

- Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya karɓi bakuncin shugaban sojin, Ibrahim Attahiru, a gidan gwamnatin jihar dake Patakwal babban birnin Rivers.

- Ya ce yana so shugaban ya kawo canji sosai a rundunar sojin domin aikin su yasha ban-ban da siyasa.

Gwamanan jihar Rivers, Nyesom Wike ya bama shugaban rundunar sojojin ƙasar nan, laftanar janar Ibrahim Attahiru, shawara kan ya janye sojojin ƙasar nan daga jikin 'yan siyasa.

KARANTA ANAN: Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace

Gwamna Wike ya faɗi haka ne ranar Talata lokacin da ya karɓi bakuncin shugaban sojojin Ibrahim Attahiru tare da kwamandan runduna ta shida dake Patakwal, janar Sani Mohammed a gidan gwamnatin jihar.

Ya ba shugaban sojojin (COAS) shawara ya kawo sabon tsari a rundunar da yake jagoranta kuma kada asa siyasa a lamarin, Punch ta ruwaito.

Matsalar Tsaro: Gwamnan Rivers yaba Shugaban Sojoji wata Muhimmiyar shawara
Matsalar Tsaro: Gwamnan Rivers yaba Shugaban Sojoji wata Muhimmiyar shawara Hoto: @GovWike
Source: Twitter

"Ƙasar nan na fuskantar matsalolin tsaro sosai, to ina bada shawara ka janye sojoji daga jikin yan siyasa saboda hakan zai ba sojojin dama suyi aikin su yadda yakamata," inji gwamnan.

KARANTA ANAN: Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

"A kwanakin baya idan kaga soja guduwa zaka yi, amma yanzun abun ya yi wahala saboda an sa sojojin cikin siyasa," Wike ya faɗa.

"Ina son ka canza tsarin domin aikin ku shine ku kare rayukan 'yan Najeriya, ku yaƙi yan fashi, 'yan ta'adda da kuma hana satar akwatin zaɓe," a cewar gwamna Wike.

A wani labarin kuma Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu

Kotun ta yanke hukunci kan gwamnatin tarayya tare da goyon bayan mai shigar da karar.

An shigar ta karar ne biyo bayan ba da wa'adin makwanni biyu na yin rajistar na NIN a kasar.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel