Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace

Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace

- Gwamnan Zamfara ya sake samun nasarar kuɓutar da mutane huɗu da aka sace a jiharsa ba tare da ya biya kuɗin fansa ba

- Waɗanda aka kuɓutar din sun bayyana cewa an sace su kwana 49 da suka wuce a garin Boko dake ƙaramar hukumar Zurmi, jihar Zamfara.

- Daga cikin waɗanda gwamnan ya kuɓutar akwai Magajin Gari da kuma kansila daga ƙaramar hukumar Zurmi

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sake samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da yan bindiga suka sace ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Waɗanda aka kuɓutar ɗin sun kasance a hannun yan bindigan tsawon kwanaki 49, kamar yadda channels TV ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Abinda Makiyaya ke yi bai dace ba, ya zama wajibi a hanasu kiwo, Inji Ɗawisu

Kuɓutattun sun bayyana cewa an sace su ne a garin Boko dake yankin ƙaramar hukumar Zurmi, jihar zamfara.

Daga cikin mutanen da gwamnan ya kuɓutar akwai Magajin Gari da kuma Kansila mai ci daga yankin karamar hukumar Zurmi.

Wannan nasara tazo ne bayan sati uku da gwamnatin jihar ta ayyana kuɓutar da wasu mutane 10 da aka sace a jihar.

Sai dai har ya zuwa yanzun babu wani cikakken bayani kan ko an bayar da kuɗin fansa ko kuma ba'a bada ba.

Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace
Gwamnan Zamfara ya ƙara samun nasarar kuɓutar da wasu mutane huɗu da aka sace Hoto: @Zamfara_state
Asali: Twitter

Idan zaku iya tunawa, a ranar 9 ga watan Maris ne kwamishin tsaro da harkokin cikin gida na jihar Zamfara, Abubakar Dauran, ya bayyana kuɓutar da wasu mutane 10 da aka sace.

KARANTA ANAN: Taƙaddama ta ɓarke a Majalisar Dattijan Ƙasar nan kan cewa Wata ƙaramar Hukuma a Arewa ta zarce Jihar Bayelsa

Ya kuma bayyana cewa mutanen sun ɗau sama da sati uku a hannun yan bindigan bayan sace su a Gwaram, ƙaramar hukumar Talatan Mafara.

Daga cikin su akwai wani mahaifin ɗaya daga cikin ɗalibai mata yan sakandire da aka sace a garin Jangeɓe.

A wancan Lokacin Dauran yace gwamnatin jihar bata biya ko sisi ba da sunan kuɗin fansa, an sako su ne bayan tattaunawar zaman lafiya.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnatin jihar zata cigaba da tattaunawar neman zaman lafiya tsakaninta da yan bindigan.

A wani labarin kuma Zulum ya sake bankado 'yan gudun hijira na bogi a sansanin Maiduguri

Gwamnan Borno, Farfesa Babagana Zulum a daren Talata ya sake bankado mutum 528 na bogi a rijistar 'yan gudun hiijira.

Lamarin ya faru ne bayan ya kai ziyarar cikin dare sansanin inda ya kirga mazauna wurin daya bayan daya da kansa.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Asali: Legit.ng

Online view pixel