Zulum da sauran gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya

Zulum da sauran gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya

- A makon nan wasu mahara da ba a san ko su waye ba suka kai hari kan tawagar gwamnan jihar Benue.

- Lamarin da ya jawo cece-kuce a bangarori daban-daban na Najeriya, tare da mayar da martanin maganganu

- Mun tattaro muku jerin gwamnonin da a tarihi tsageru suka taba kai musu hari a Najeriya

Biyo bayan hare-haren da ake kai wa al'umomi daban-daban a wasu yankunan jihohi musamman arewacin Najeriya, lamarin ya kara karfi yayin da aka hari tawagar motocin gwamnan jihar Benue.

Wannan abin takaici ba a kan gwamnan Benue kadai ya taba faruwa ba, a tarihi an samu hare-hare kan wasu gwamnoni, ciki har da na watannin baya a jihar Borno.

Mun tattaro muku jerin gwamnonin da tsagerun maharan suka kaiwa hari, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA: APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

1. Tsohon Gwamnan Benue George Akume

Jerin gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya
George Akume, Tsohon Gwamnan Jihar Benue | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

A ranar 3 ga Maris shekarar 2004 ’yan bindiga suka far wa ayarin motocin tsohon Gwamnan Benue, George Akume, inda suka kashe wani a motar tare da raunata wani.

2. Tsohon gwamnan Borno Kashim Shettima

Jerin gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya
Kashim Shettima, Tsohon Gwamnan Jihar Borno | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

'Yan ta'addan Boko Haram a ranar 13 ga Fabrairun shekarar 2019 sun kai hari kan ayarin motocin tsohon Gwamnan Borno Kashim Shettima.

Shettima na kan hanyarsa ta zuwa taron siyasa daga Gamboru zuwa Ngala da ke jihar lokacin da harin ya afku.

KU KARANTA: An ba da belin mawakin yabo da ya sake wakar yabo da ba a tantance ba

3. Gwamnan Borno Babagana Zulum

Jerin gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya
Farfesa Babagana Umaru Zulum, Gwamnan Jihar Borno | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Mutum 18 sun mutu a ranar 26 ga Satumban shekarar 2020 lokacin da ‘yan ta’addan Boko Haram suka yi wa ayarin motocin Gwamnan Borno Babagana Zulum kwanton bauna.

Sojoji hudu, 'yan anda 10 da fararen hula hudu sun halaka yayin harin/kwanton baunar, wanda daga bisani mayakan sojojin Najeriya suka fatattake 'yan ta'addan.

4. Gwamna Samuel Ortom

Jerin gwamnoni 4 da tsageru suka taba kaiwa hari a Najeriya
Sameul Ortom, Gwamnan Jihar Benue | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Wasu da ake zargin makiyaya ne a ranar Asabar 20 ga Maris din bana (2021), sun kai hari kan ayarin motocin Gwamnan Benue, Samuel Ortom.

Lamarin, a cewar wani jami'in gwamnati, ya faru ne a Tyo Mu da ke hanyar Makurdi/Gboko.

An kuma tattaro cewa Gwamnan na kan hanyarsa ta zuwa Makurdi, babban birnin jihar lokacin da wadanda ake zargin makiyayane suka bude wuta kan ayarin motocinsa amma sai jami'an tsaro suka fatattake su.

A wani labarin daban, Wata kungiyar Fulani da ke ikirarin kare muradin Fulanin (FUNAM), ta ce ita ke da alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue, PM News ta ruwaito.

A cikin wata sanarwa da aka bai wa manema labarai, wanda aka yi kuskuren rubuta sunan Ortom sau da yawa, kungiyar ta ce manufarta ita ce kashe Ortom.

Ta sha alwashin hallaka Ortom, saboda kamar yadda ta yi ikirarin, yana adawa da Fulani.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.