Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu

Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu

- Babbar kotun tarayya da ke Legas ta kammala sauraren kara kan wa’adin yin rajistar NIN

- Kotun ta yanke hukunci kan gwamnatin tarayya tare da goyon bayan mai shigar da karar

- An shigar ta karar ne biyo bayan ba da wa'adin makwanni biyu na yin rajistar na NIN a kasar

Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Legas ta ba da umarnin kara wa’adin rajistar lambar shaidar dan kasa (NIN).

A cewar jaridar Vanguard, kotun a wani hukunci ta bayyana cewa ya kamata a tsawaita rajistar tsawon watanni biyu daga ranar Talata, 23 ga Maris, 2021.

KU KARANTA: Sojojin Najeriya sun yi kaca-kaca da haramtacciyar matatar mai a Abia

An yanke hukuncin ne dangane da karar da wani lauya mai kare hakkin dan Adam, Monday Ubani, ya shigar a kan gwamnatin tarayya, Hukumar Sadarwa (NCC), da Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki.

Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu
Kotu ta bada umarnin tsawaita wa'adin rajistar NIN zuwa watanni biyu Hoto: koko.ng
Asali: UGC

Mai gabatar da karar ya ce da farko makonni biyu (da yanzu aka kara zuwa 6 ga Afrilu, 2021) da aka bai wa kamfanonin sadarwar don toshe layukan 'yan Najeriyan da ba su lika su da NIN ba ya keta hakkin 'yancin fadin albarkacin baki, mallakan kadarori masu motsi da ma na rayuwa.

Lauyan, saboda haka, ya roki kotun da ta ba ta umarnin dakatar da wannan wa’adi da kara wa’adin, kamar yadda jaridar This Day ta ruwaito.

A martaninta, alkalin kotun, Mai shari’a Maureen Onyetenu ta amince da bukatar mai karar ta hanyar ba da umarnin a kara lokacin aikin.

KU KARANTA: APC na da shirin ci gaba da rike madafun iko na tsawon shekaru 32, in ji Buni

A wani labarin, Karamar Ministar Masana'antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Mariam Katagum, a ranar Litinin ta ce tun daga farkon wadanda suka fara cin gajiyar shirin a ranar 17 ga Janairun 2021, an amince da biyan jimilar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin Survival Fund a fannin sufuri.

Wannan na fitowa ne daga wata sanarwar babban mataimaki na musamman ga mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai ya fitar a wasu tarurruka da aka gudanar na shirin, jaridar Punch ta ruwaito.

Sanarwar ta bayyana cewa, “Jimillar mutane 155,920 da za su ci gajiyar shirin a fannin sufuri ya zuwa yanzu an amince da a biya su yayin da har yanzu mutum 9,109 ke jiran tantacewa don biya.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.