Dole APC ta tattara komatsanta nan da 2023, PDP tayi wa Buni martani

Dole APC ta tattara komatsanta nan da 2023, PDP tayi wa Buni martani

- Jam'iyyar PDP ta sha alwashin cewa jam'iyyar APC za ta tattara komatsanta ta bar mulki nan da 2023

- Kakakin jam'iyyar APC ya sanar da haka ne bayan Gwamna Buni yace sai APC ta kara shekaru 26 a karagar mulki

- PDP tace 'yan Najeriya ba za su cigaba da zama cikin fatara, yunwa, kunci, rashin tsaro da wahala mara karewa ba

Jam'iyyar PDP ta kwatanta abinda jam'iyyar APC tace da shirme tare da adawa ga dukkan 'yan Najeriya.

Shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Talata yace jami'iyyarsa za ta cigaba da mulki nan da shekaru 26 masu zuwa.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, a yayin martani ga wannan ikirarin, kakakin jam'iyyar PDP, Kola Ologbondiyan, yace tuni 'yan Najeriya suka kai karshen hakurin da za su iya dasu kuma sun shirya fatattakarsu nan da 2023.

"Jam'iyyar PDP ta kwatanta ikirarin da APC tayi, na yi wa 'yan Najeriya miliyan 36 rijista a matsayin salon siyasa da kuma karyar da suka saba, wacce ba za ta iya sauya ra'ayin 'yan Najeriya ba.

KU KARANTA: NDLEA ta Bankado Wata Tafkekiyar Gonar Wiwi a Jihar Kano

Dole APC ta tattara komatsanta nan da 2023, PDP tayi wa Buni martani
Dole APC ta tattara komatsanta nan da 2023, PDP tayi wa Buni martani. Hoto daga @daily_trust
Source: Twitter

KU KARANTA: Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu

"Jam'iyyar PDP ta san cewa shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC, Gwamna Mai Mala Buni yayi wannan ikirarin ne a tunaninsa cewa tsoratar da INEC, ma'aikatar shari'a da kuma jami'an tsaro tare da samo 'yan daba da suka saba yi daga kasashe masu makwabtaka, za su taimaka wurin sauya ra'ayin 'yan Najeriya a zabuka masu zuwa.

"A rashin tunanin Buni, 'yan Najeriya su cigaba da mika kansu cikin wasu shekaru 26 na kunci, azaba, yunwa, rashin tsaro da kuma wahala mara karewa. Wannan shine babban ganganci, rashin tunani da rainin da ake wa 'yan Najeriya," Ologbondiyan yace.

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karba bakuncin Oladimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai da Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun a fadarsa dake Abuja.

Bankole da Daniel cikin kwanakin nan ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Yayin kai ziyarar fadar shugaban kasa, sun samu rakiyar Mai Mala Buni, Mohammed Badaru da Atiku Bagudu, gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit

Online view pixel