Shugaba Buhari ya karba bakuncin sabbin 'yan APC, Daniels da Bankole a fadarsa

Shugaba Buhari ya karba bakuncin sabbin 'yan APC, Daniels da Bankole a fadarsa

- Shugaba Buhari ya karba bakuncin tsohon gwamnan jihar Ogun da tsohon kakakin majalisar wakilai

- Daniels Gbenga da Oladimeji Bankole, sun kaiwa shugaban kasa ziyara a fadarsa dake Aso Rock a Abuja

- Sun kai ziyarar a ranar Litinin bayan cikin kwanakin nan sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya karba bakuncin Oladimeji Bankole, tsohon kakakin majalisar wakilai da Gbenga Daniel, tsohon gwamnan jihar Ogun a fadarsa dake Abuja.

Bankole da Daniel cikin kwanakin nan ne suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Yayin kai ziyarar fadar shugaban kasa, sun samu rakiyar Mai Mala Buni, Mohammed Badaru da Atiku Bagudu, gwamnonin Yobe, Jigawa da Kebbi.

Daniels yayi shugabancin jihar Ogun daga 1999 zuwa 2007, yayin da Bankole ya rike mukamin kakakin majalisar wakilai daga 2007 zuwa 2011 duk a karkashin jam'iyyar adawa ta PDP.

KU KARANTA: Alaka da ƴan bindiga: Matawalle ya rantse da Qur'ani, ya bukaci ƴan jiharsa da su yi

Shugaba Buhari ya karab bakuncin sabbin 'yan APC, Daniels da Bankole a fadarsa
Shugaba Buhari ya karab bakuncin sabbin 'yan APC, Daniels da Bankole a fadarsa. Hoto daga @BuhariSallau1
Asali: Twitter

KU KARANTA: Da duminsa: INEC ta dakatar da zaben maye gurbi na Ekiti saboda zubda jini

Karin bayani na nan tafe...

A wani labari na daban, Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom a ranar Asabar yayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jami'an tsaro da su tsamo ƴan ta'addan da suka addabi jiharsa.

Ortom yayi magana da manema labarai bayan tsallake harin da ake zargin makiyaya ne suka kai masa a garin Makurdi.

Channels Tv ta ruwaito cewa, ya je kai ziyara wata gona yayin da maharan suka far masa amma jami'an tsaro dake tare da shi sun yi nasarar fatattakarsu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel