Fani Kayode ya musanta cin zarafin ma'aikatansa na cikin gidansa, ya garzaya gaban kotu
- Rikicin Femi Fani Kayode da tsohuwar matarsa, Precious Chikwendu, ya cigaba da yawo a kafafen sada zumunta
- A makon da ya gabata ne wani bidiyon mai raino a gidansa wanda yake bayyana tsananin zalincinsa da muguntarsa yayi ta yawo
- Saidai ɗan siyasar ya ce sam ba gaskiya bane bidiyon, an shirya shi ne musamman don a ɓata masa sunansa kuma ba zai yarda ba
Tun bayan rikicin tsohon ministan sufurin jiragen sama, Femi Fani Kayode da tsohuwar matarsa, Precious Chikwendu, ya fallasa a idon duniya, bayan mutuwar aurensu ake ta daga akan wanda zai riƙe yaransu guda hudu, tsakanin shi da matarsa.
A ranar Juma'ar data gabata, 19 ga watan Maris aka sake ganin wani bidiyon ministan da yayi ta yawo a kafafen sada zumunta wanda yake nuna tsananin muguntarsa.
Bidiyon da ya janyo cece-kuce iri-iri a kafafen sada zumunta kamar yadda aka ga Fani-Kayode riƙe da guduma yana tsoratar da wani ma'aikacinsa na gida akan ya yi masa laifi kamar zai buga masa gudumar.
KU KARANTA: Hoton matashin bature sanye da kayan NYSC ya janyo cece-kuce
KU KARANTA: Onnoghen: Buhari ya fattakeni ne bayan an ce masa na gana da Atiku a Dubai
Fani-Kayode ya musanta zargin da ake masa na cutar da makusantansa kuma ya lashi takobin maka duk wanda yake da hannu a yada wannan mummunan labari akansa zuwa kotu.
A wani labari na daban, Dino Melaye, tsohon sanatan da ya wakilci jihar Kogi ta yamma, yace babbar damfarar da ta taba faruwa a Afrika shine yadda aka goyawa Buhari baya ya samu shugabancin kasa a 2015.
Melaye ya sanar da hakan ne a ranar Juma'a yayin da ya bayyana a wani shiri na gidan talabijin na Channels.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, Melaye, wanda yanzu dan babbar jam'iyyar adawa ce ta PDP, ya bar jam'iyyar APC a shekarar 2018.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng