Hajji 2021: Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari

Hajji 2021: Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari

- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya kirayi maniyyatan hajjin bana da su zama jakadun ƙasar nan nagari a lokacin gudanar da aikin.

- Gwamnan ya yi wannna kira ne a ya yin da yake jawabi a wajen buɗe taron bita da ƙara wa juna sani da aka shiryawa mahajjatan bana, 2020/2021

- A cewarsa, yana fatan mahajjatan Kano su zama masu kyawawan ɗabi'u a ya yin gudanar da aikin su.

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya yi kira ga mahajjatan bana na jihar Kano da su zama wakilan ƙasar nan nagari, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a ya yin jawabinsa a wajen buɗe taron ƙarawa juna sani da aka shirya ma mahajjatan bana a jihar, 2020/2021.

KARANTA ANAN: Najeriya na cikin halin kakanikaye, Ministan Tsaro Bashir Magashi

Gwamnan wanda sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, ya wakilta yace an shirya taron ne saboda a haskaka ma mahajjata da ilimantar dasu akan yadda ake aikin hajji a addinance.

Ya kuma ƙara da cewa muna fatan maniyyatan mu zasu yi abun da zai haskaka kasar mu a lokacin da suke a ƙasa mai tsarki.

Hajji 2021: Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari
Hajji 2021: Gwamna Ganduje ya yi kira ga Maniyyata su zama Jakadun ƙasa nagari Hoto: @GovUmarGanduje
Source: Twitter

"Muna fatan maniyyata aikin hajjin bana zasu zama masu kyawawan ɗabi'u a lokacin gudanar da aikin su." inji shi.

KARANTA ANAN: Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi

A ɓangarensa, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Bayero, ya bayyana cewa: "Ko kaɗan bamu ji daɗin rashin samun damar yin aikin hajji ba a shekarar 2020 saboda ɓullar annobar COVID19."

Daga ƙarshe, sakataren hukumar kula da jin daɗin alhazai na jihar Kano, Alhaji Muhammed Dambatta, ya yabawa gwamnatin jihar bisa goyon bayan da take bawa hukumar sa.

A wani labarin kuma Zamu Kama Duk Wani Matafiyi mai dauke da Gwajin COVID19 na Bogi, NCDC

Hukumar NCDC ta bayyana cewa zata cafke duk wani matafiyi da ta kama ɗauke da sakamakon gwajin cutar korona na bogi

Shugaban Hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka a taron kwamitin yaƙi da cutar korona a Abuja.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.

Source: Legit

Online view pixel