Najeriya na cikin halin kakanikaye, Ministan Tsaro Bashir Magashi
- Ministan tsaron Najeriya ya bayyana shirin da gwamnatin tarayya keyi na kawo karshen matsalar tsaro
- Najeriya ta shiga cikin wani mugun hali kuma abubuwa da dama na barazana ga rayuwar kasar, cewarsa
- Shugaban hafsan tsaro ya bayyana abinda zasu yi daga yanzu
Gwamnatin tarayya a ranar Litinin ta bayyana cewa an kammala shirye-shiryen fito-na-fito da yan ta'addan dake kokarin ganin bayan Najeriya.
Ya ce Najeriya za tayi amfani da karfin Soja wajen dakile shirin da suke yi na ruguza kasar.
Wannan na zuwa ne lokacin shugaban hafsoshin tsaro, Janar Lucky Irabor, ya lashi takobin hallaka duk wani mai dauke da makami a cikin dazuka domin tabbatar da tsaro a fadin tarayya.
Ministan Tsaro, Manjo Janar Bashir Magashi (mai murabus) ya yi jawabi a shirin kwana daya da aka shirya a Abuja mai taken 'Inganta karfin Soja wajen yakin da ta'addanci a Najeriya.'
Janar Magashi ya bayyana cewa Najeriya na cikin halin kakanikaye sakamakon hare-haren yan ta'adda, yan bindiga, da masu garkuwa da mutane.
A cewar Magashi, gwamnatin tarayya shirye take da kare rayuka da dukiyoyin yan Najeriya bisa umurnin shugaban kasa ga hafsoshin tsaro.
"Muna cikin halin kakanikaye kuma muna bukatar fahimtar juna, goyan baya da hadin kai da masu ruwa da tsaki," Ministan yace.
Ya kara da cewa rashin tsaro na barazana ga abubuwa da yawa wanda ya hada da lamarin siyasa, rashin cigaba, rabuwar kai, harkar noma.
DUBA NAN: Ganduje: Harin da aka kai wa Gwamnan Benuwai ya kada hanjin sauran Gwamnonin Jihohi
KU KARANTA: Sojoji za su yi luguden wuta na ‘mai uwa da wabe, za a kashe duk wanda ke cikin daji
A bangare guda, shugaban hafun sojojin Najeriya, Janar Lucky Irabor ya ce dakarunsa sun kammala shirin ganin bayan ‘yan bindigan da ke kawo rashin zaman lafiya.
Da yake magana wajen taron da aka shirya a Abuja a kan sha’anin tsaro, Janar Lucky Irabor, ya ce za su bankado duk wadanda su ka fake a jeji su na ta’adi.
Daily Trust ta rahoto Lucky Irabor ya na cewa za a samu zaman lafiya nan ba da dadewa ba a kasar nan.
Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.
Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.
Asali: Legit.ng