Zamu Kama Duk Wani Matafiyi mai dauke da Gwajin COVID19 na Bogi, NCDC
- Hukumar NCDC ta baygana cewa zata cafke duk wani matafiyi da ta kama ɗauke da sakamakon gwajin cutar korona na bogi
- Shugaban Hukumar Chikwe Ihekweazu ya bayyana haka a taron kwamitin yaƙi da cutar korona a Abuja.
- Yace sun gano wani ɗakin gwaje-gwaje da ke ɗaukar nauyin bada wannan sakamakon kuma sun rufe shi
Hukumar kiyaye yaɗuwar cututtuka ta ƙasa (NCDC) ta ce duk wani matafiyi da aka samu da sakamakon gwajin korona na bogi za'a kama shi kuma zai fuskanci hukunci.
Shugaban hukumar NCDC, Chikwe Ihekweazu, ya bayyana haka ya yin da yake jawabi a taron kwamitin yaƙi da cutar COVID19 ranar Litinin.
KARANTA ANAN: Yan bindigan da suka sace Sarkin Gargajiya A Jihar Ogun sun Buƙaci a basu 100 Miliyan
Shugaban ya ce an ƙaddamar da shafi na musamman don tabbatar sakamakon gwajin.
Jaridar The Cable ta ruwaito cewa, wasu matafiya na biyan jami'an gwamnati kuɗi don su basu sakamakon gwajin na ƙarya.
Bayan wannan rahoto ne, gwamnatin tarayya ta binciko ɗakin gwajin dake wannan aikin kuma ta rufe shi.
Ihekweazu ya ƙara jaddada cewa duk wani matafiyi da yazo da gwajin ƙarya filin sauka da tashin jiragen sama za'a cafke shi kuma za'a hukunta shi.
Haka zalika, shugaban ya ce daga yanzu duk wani gwaji da aka yi a ɗakin gwaji mai zaman kanshi sai jami'an lafiya na filin jirgi sun bincike shi.
"Da yawa daga cikin ku kunji maganar da nayi a baya kan shafin tantance sakamakon gwajin korona, to wannan shafin ya fara aiki yanzu," Ihekweazu ya faɗa.
"A satin da ya gabata, mun miƙa matafiya da yawa ga hukumonin tsaro saboda kama su da sakamon gwajin bogi da muka yi."
KARANTA ANAN: Kamfanin MTN ya bai wa Najeriya gudunmawar alluran Korona guda 300,000
"Wani lokacin jami'an mu ne ke bada wannan sakamakon na ƙarya, amma daga yanzin duk wanda muka kama to ya kuka da kansa."
Ya ƙara da cewa: "Muna ba yan Najeriga shawara, duk wanda zai yi tafiya zuwa wata ƙasa to ya tabbatar ya yi gwajin COVID19 a wuraren da aka amince da su wanda za'a iya gani a shafin mu na yanar gizo."
"Kafin ka yi tafiya, ka duba ƙasar da zaka idan suna da buƙatar sakamakon dole, to ka garzaya ka yi a wuraren da aka amince da su, domin zaka samu sakamakon da aka amince da shi a ko ina. Hakan yana da matukar amfani."
A wani labarin kuma EFCC za ta binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi karfinsu a shafukan sada zumunta
Mataimakiya ga shugaban kasar Najeriya kan kafofin sada zumunta, Laurette Onochie, ta ce hukumomin da ke yakar cin hanci da rashawa wato EFCC da ICPC za su binciki 'yan Najeriya da ke rayuwar da ta fi ƙarfinsu musamman a shafukan sada zumunta.
Wannan ya biyo bayan umarnin da shugaban EFCC ya bayar na bincikar ma'aikatan banki.
Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.
Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.
Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77.
Asali: Legit.ng