Rikicin Cikin Gida: PDP ta kori wasu manyan Shugabannin ta a Jihar Katsina

Rikicin Cikin Gida: PDP ta kori wasu manyan Shugabannin ta a Jihar Katsina

- Jam'iyyar PDP a ƙaramar hukumar Matazu dake jihar Katsina ta kori shugabanta da kuma shugabar mata.

- PDP ta yanke wannan hukuncin ne bayan kama su da laifin yin zagon ƙasa ga jam'iyyar a matsayinsu na shuwagabanni

- A cewar shugaban kwamitin riko, an basu damar kare kansu akan tuhumar da aka yi musu amma suka kasa

Jam'iyyar PDP ta kori manyan shuwagabannin ta guda biyu a jihar Katsina, waɗanda abun ya shafa sune, shugaban jam'iyyar PDP, da shugabar mata ta jam'iyyar a karamar hukumar Matazu dake jihar ta Kastina.

KARANTA ANAN: Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari

Shugaban jam'iyyar na riƙon ƙwarya, Alhaji Jabir Adamu, ya bayyana haka jim kaɗan bayan fitowa taron masu ruwa da tsaki a PDP wanda ya gudana a ƙaramar hukumar ta Matazu.

Ya kuma bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne bayan gano cewa suna ma jam'iyyar zagon ƙasa lokacin da PDP ta gudanar da babban taronta a Matazu kwanan nan.

Adamu ya ƙara da cewa an ɗauki matakin ne a taron da PDP ta yi da mambobinta da kuma shuwagabannin gundumominta dake faɗin ƙaramar hukumar, jaridar PM News ta ruwaito.

Rikicin Cikin Gida: PDP ta kori wasu manyan Shugabannin ta a Jihar Katsina
Rikicin Cikin Gida: PDP ta kori wasu manyan Shugabannin ta a Jihar Katsina Hoto: @PDP_2023
Source: Twitter

"'Yayan jami'iyyar sun nuna rashin jin daɗin su kan yadda tsohon shugaban da tsohuwar shugabar mata suke gudanar da aikace-aikacen jami'iyyar." inji Adamu.

KARANTA ANAN: 'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

"Basu tafiya da kowa ya yin gudanar da ayyukan PDP ɗin. Duk da ambasu dama su bayyana dalilan su na yin haka amma suka ƙi, hakan yasa aka gudanar da zaɓe akan su daga ƙarshe aka kore su." a cewarsa.

Taron ya samu halartar dukkanin shuwagabannin jam'iyyar harda shi kanshi shugaban da aka kora.

A wani labarin kuma APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal yace bayyi mamaki ba dan jam'iyyar APC bazata shiga zaɓen kananan hukumomin jihar da aka shirya za'ayi ranar 27 ga watan Maris ba, a gaba ɗaya ƙananan hukumoni 23 da jihar ke dasu.

A cewarsa jam'iyyar ta APC bata da abinda zata tunkari jama'a dashi saboda ta kasa cika alƙawurran da tayi.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Source: Legit

Online view pixel