Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari

Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari

- Arewa Youth Federation ta na da ja a kan harin da aka kai wa Samuel Ortom

- Kungiyar Arewan ta ce sam babu hujjar da ke nuna an kai wa Gwamnan hari

- AYF ta kalubalanci Gwamnan Benuwai ya fito da hujjar harin da aka kai masa

Kungiyar Arewa Youth Federation (AYF) ta jefa wa gwamnan jihar Benuwai, Mista Samuel Ortom, kalubale a game da harin da ya ke cewa an kai masa.

Arewa Youth Federation ta bukaci gwamna Samuel Ortom ya fito da hujjojin da za su nuna makiyaya Fulani ne su ka kai masa hari a ranar Asabar.

Samuel Ortom ya fito ya fada wa Duniya Fulani ne su ka nemi su ga karshen rayuwarsa, ya ce ‘yan Miyetti Allah Kautal sun yi barazanar ganin bayansa.

KU KARANTA: Ortom: Za ayi bincike - Shugaban kasa Muhammadu Buhari

Amma shugaban kungiyar Arewa Youth Federation, Adamu Kabir Matazu, ya na da ta-cewa a game da wannan ikirari da Mai girma Samuel Ortom ya yi.

Daily Trust ta rahoto Alhaji Adamu Kabir Matazu ya na mamakin yadda Ortom ya cin ma wannan matsaya.

Matazu ya ce: “Mun ga hare-hare a kan gwamnoni kamar lokacin da aka ga ‘Yan Boko Haram sun kai wa tawagar gwamnan Borno, Babagana Zulum hari.”

A game da harin da ake cewa an kai wa Zulum, Adamu Kabir Matazu, ya ce babu wata hujja a kasa.

Kungiyar Arewa ga Ortom: Ka fito da hujjar da za ta nunawa Duniya Fulani sun kai maka hari
Samuel Ortom a fadar Shugaban kasa Hoto: www.saharareporters.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ortom ya bukaci Buhari yayi maganin ƴan ta'addan Benuwai

Shugaban na Arewa Youth Federation ya ce akwai shakku game da batun kai wa gwamnan hari, ballatana a daura laifin a kan Fulani ba tare da wata hujja ba.

“Amma Ortom bai gabatar da wasu hujjoji ba. Ana samun bata-gari a kowane bangare a al’umma, babu hujjar da ke nuna an kai masa hari, har ma ace makiyaya Fulani ne.”

Kun samu labarin cewa wata kungiyar Fulani ta fito ta yi ikirarin ita ce ta kai wa gwamnan jihar Benuwai Benuwai hari, ta ce ta so ne ta hallaka Samuel Ortom.

FUNAM mai rajin kare muradin Fulani ta ce alhakin yunkurin kashe Gwamna Samuel Ortom ya na kanta, dalilinta shi ne gwamnan ya na adawa da kabilar.

Kungiyar ta ce: “Duk inda kuka kasance, matukar kun nuna wa Fulani adawa, za mu durkushe ku."

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel