APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto

APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto

- Gwamnan Sokoto ya ce ko kaɗan baiyi mamakin cewa APC baza ta shiga zaɓen ƙananan hukumomin jihar ba

- A cewarsa jam'iyyar ta APC bata da abinda zata tunkari jama'a dashi saboda ta kasa cika alƙawurran da tayi

- Anashi ɓangaren, shugaban PDP na jihar ya bayyana cewa kimanin yan APC 12,000 ne suka dawo PDP

Gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal yace bayyi mamaki ba dan jam'iyyar APC bazata shiga zaɓen kananan hukumomin jihar da aka shirya za'ayi ranar 27 ga watan Maris ba, a gaba ɗaya ƙananan hukumoni 23 da jihar ke dasu.

KARANTA ANAN: Wata sabuwa: Tsagerun Neja-Delta su na neman su fatattaki kamfanonin da ke aikin hako fetur

Tambuwal, a yayin ƙaddamar da kamfen din jami'iyyar sa ta PDP a ƙaramar hukumar Gwadabawa Yace:

"Ban yi mamaki ba dan jam'iyyar APC ta jihar ta yanke cewa ba zata shiga zaɓen ba saboda APC ta rasa karsashin ta a idanun jama'a akan rashin cika alƙawurran da ta ɗauka."

"Sun san basu yi komai ba, kuma basu da abinda zasu iya a jihar," inji shi.

Gwamnan ya yi kira ga masu goyon bayan PDP da su fito ranar zaɓe su zaɓi ɗan takarar jam'iyyar PDP, ya kuma bayyana muhimmancin ƙananan hukumomi cewa sune suka fi kusa da jama'a, jaridar Punch ta ruwaito.

APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto
APC ba zata shiga zaɓen ƙananan hukumomi ba a Jihar Sokoto Hoto: @AWtambuwal
Asali: Twitter

KARANATA ANAN: Barnar tsuntsaye ta ja jirgin sama da zai je Legas saukar gaggawa a Kano

"Zaɓen yana da muhimmanci kuma yasha banban da sauran. Ku zaku fito da kanku kuyi zaɓe. Wannan zaɓen yana da muhimmanci saboda zai baku dama ku zaɓi shuwagabannin ku waɗan da kuke so." inji gwamnan.

Shugaban jam'iyyar PDP na jihar Sokoto, Bello Goronyo, ya miƙa ma yan takarar jam'iyyar PDP 12 tutar jami'iyyar waɗanda zasu fafata a zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi. Sannan kuma ya sanar da mutane 12,000 daga jam'iyyar APC da suka sauya sheƙa zuwa PDP.

A wani labarin kuma 'Yan Sanda Sun Cafke Gungun Masu Garkuwa da Mutane A Adamawa

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta bayyana nasarar cafke wasu mutane da ake zargin suna da hannu wajen satar mutane da kuma fashi da makami a jihar.

Ana zargin mutanen da hana al'umma sakat a bodar data haɗa Najeriya da ƙasar Kamaru.

Ahmad Yusuf sabon ma'aikacin legit.ng ne ɓangaren Hausa, ya fara aiki kwa nan nan. Yana kawo rahotanni a ɓangare daban-daban.

Ya yi karatun digirinsa na farko a Jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil jihar Kano . Kuma yana da burin ƙwarewa a aikin jarida.

Za'a iya samunsa a dandalin sada zumunta na twitter @ahmadyusufmuha77 .

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel