'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya

- Wasu sojojin kasar Kamaru sun rasa rayukan su a Najeriya sakamakon harin Boko Haram

- Majiya daga sojojin Najeriya sun tabbatar da faruwar lamarin a wani yankin jihar Borno

- Mayakan Boko Haram sun afkawa rundunar sojojin ne dauke muggan makamai a yankin

Sojojin Kamaru biyu da aka tura zuwa Najeriya sun mutu da yammacin ranar Asabar a wani harin Boko Haram a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar, in ji majiyar sojojin Najeriya a ranar Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Masu tayar da kayar bayan, tafe a kafa da kuma a cikin manyan motocin da ke dauke da muggan makamai, sun afka wa sojojin Najeriya a wajen garin Wulgo. Hakanan an kaiwa sojojin Kamaru hari bayan girke su daga ketaren iyaka don taimakawa rundunar.

KU KARANTA: Burutai da sauran hafsoshin tsaro za su bayyana a gaban majalisa kan batun kudin makamai

'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya
'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojojin Kamaru a Najeriya Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

"Sojojin CDF (Dakarun Tsaron Kamaru) biyu sun mutu a musayar wuta na tsawon minti 40 tare da 'yan ta'addan Boko Haram," in ji majiyar sojojin Najeriya.

"Wasu sojojin CDF guda uku da wani sojan Najeriya sun ji rauni a fafatawar," in ji jami'in sojan, daga wata majiyar sojan Najeriya ta biyu ta tabbatar.

Wata motar sulke ta sojojin Najeriya da manyan motocin Boko Haram guda biyu sun lalace a yayin artabun yayin da "da yawa" daga Boko Haram suka mutu, in ji jami'in sojan na biyu.

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da harin ne daga dajin Wulgo da ke kusa, wani sanannen maboyar Boko Haram.

KU KARANTA: Kungiyar gwamnonin Najeriya sun Allah wadai da harin da aka kai wa gwamnan Benue

A wani labarin daban, Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta samu nasarar kashe wasu 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Dikwa a jihar Borno, BBC Hausa ta ruwaito.

Cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kakakin rundunar Mohammed Yerima wanda ya fitar a ranar Laraba, ya ce rundunar ta samu wannan nasara ne tare da hadin gwiwar wasu 'yan sintiri a yammacin ranar Litinin.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel